A gun taron koli na ministoci mata na duniya, da aka shirya a ran 5 ga wata a birnin Hanoi, a madadin taron koli ne, shugabar kwamitin da ke kula da harkokin taron kolin na wannan karon, Madam Irene Natividad ta nuna tausayi da jejeto ga mata da yara na kasar Sin da suke shan wahalar girgizar kasa.
Madam Natividad ta ce, taron koli ya yanke shawarar ba da taimakon kudi na karo na farko da yawansu ya kai kudin Amurka dala dubu 5 ga yankunan da ke fama da girgizar kasa, domin taimakawa mata da yara na wadannan yankuna. Ban da wannan kuma, taron koli ya kaddamar da wani asusu domin ci gaba da neman kudin kyauta da aka bayar. A sa'i daya kuma, Madam Natividad ta yi kira ga dukkan mahalartan taron da su bayar da kudin kyauta cikin yakini.
Shugabar tawagar wakilai ta kasar Sin, kuma mataimakiyar ministan kasuwanci ta kasar Sin Madam Ma Xiuhong ta nuna godiya cikin sahihiyar zuciya ga goyon baya da kuma kudin kyauta da taron koli ya bai wa kasar Sin.(Danladi)
|