Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-05 20:43:43    
Kasar Sin ta soma gudanar da ayyukan tsare-tsaren shirin sake raya yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa

cri
Yau 5 ga wata, Mr. Qi Ji, mataimakin ministan harkokin gidaje da raya birane da kauyuka na kasar Sin, ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, an riga an soma gudanar da ayyukan tsare-tsaren shirin sake raya yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa a karkashin jagorancin ma'aikatar harkokin gidaje da raya birane da kauyuka na kasar, da hukumomin da abin ya shafa.

A gun taron manema labaru da aka shirya a wannan rana, Mr. Qi Ji ya ce, ayyukan tsare-tsaren shirin sake raya yankuna masu fama da bala'in na kunshe da aikin tsare-tsare a fannin gine-ginen garuruwa, da kauyuka, da dai sauransu. (Bilkisu)