Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-05 19:46:55    
Sin za ta tabbatar da yin amfani da gudummawar da aka bayar a wajen jama'ar da girgizar kasa ta galabaitar da su

cri

A gun taron manema labarai da ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya kira a jiya 4 ga wata, an bayyana yadda kasar Sin ke karbar gudummawar da kasashen duniya suka ba ta bayan da babbar girgizar kasa ta afkawa lardin Sichuan. A gun taron, jami'an kasar Sin sun bayyana cewa, Sin za ta dauki matakai, don tabbatar da yin amfani da gudummawar da aka samu daga gida da waje wajen taimakon jama'ar da bala'in ya galabaitar da su. A sa'i daya kuma, Sin na maraba da kasashen duniya da su ba ta taimako da tallafi wajen farfado da yankunan da bala'in ya shafa.

A gun wannan taro da aka yi a ran 4 ga wata, Mr.Wang Zhenyao, shugaban sashen kula da ayyukan agaji na ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar Sin, ya bayyana cewa, ya zuwa ran nan da karfe 12, gaba daya Sin ta karbi kudade da kayayyakin agaji da yawansu ya wuce kudin Sin yuan biliyan 43 da miliyan 600 daga gida da waje, ciki har da kudade da kayayyakin da yawansu ya kai kimanin kudin Sin yuan biliyan 4 da miliyan 700 da gamayyar kasa da kasa suka ba ta. Mr.Wang Zhenyao ya kuma yi alkawarin cewa, Sin za ta tabbatar da yin amfani da kudaden da kayayyakin wajen taimakon jama'ar da girgizar kasa ta galabaitar da su.


1 2