Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-05 17:27:03    
Sin za ta tabbatar da yin amfani da gudummawar da aka bayar a wajen jama'ar da girgizar kasa ta galabaitar da su

cri

A cewar Mr.Wang Zhenyao, don kulawa da gudummawar da aka bayar yadda ya kamata, ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar Sin ta bayar da ka'idoji dangane da yadda za a kula da su da kuma yi amfani da su, ta kuma kafa tsari mai inganci, don yin amfani da kudaden da kayayyakin a fili kuma a bayyane. Ya kuma kara da cewa, sassan kula da harkokin jama'a suna son hada gwiwa da masu ba da gudummawa wajen sa ido a kan yadda ake yin amfani da kudade da kayayyakin agaji.Ya ce,"Kasashe daban daban, ciki har da kungiyoyin jama'a iri daban daban na kasar Sin da masu ba da agaji, idan suna son bin yadda ake yin amfani da gudummawarsu, to, za mu yi kokarin hada gwiwa da su. Muna fatan gudummawarsu za ta gamsar da su kansu."

A gun taron kuma, shugaban sashen kula da harkokin kasa da kasa na ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin, Mr.Zhang Kening ya ce, yadda gwamnatin kasar Sin ke karbar gudummawar kasashen duniya a fili kuma a bayyane, ya sami yabo daga gida da waje gaba daya. A lokacin da ake farfado da yankunan da bala'in ya shafa, Sin za ta ci gaba da daukar irin wannan matsayi, kuma tana maraba da kasashen duniya da su ba ta taimako wajen farfado da yankunan da girgizar kasa ta shafa. Ya ce,"Misali, farfado da kayayyakin amfanin jama'a, ciki har da asibitoci da makarantu da na'urorin jin dadin jama'a da kuma muhalli, dukan wadannan fannoni za su kasance fannonin da za mu nuna fifiko wajen hada gwiwa da hukumomin agaji na kasashen duniya. Muna fatan a lokacin da muke farfado da yankunan da bala'in ya shafa, za mu yi cikakken amfani da gudummawar, don ba da taimako ga farfado da ayyukan ba da ilmi da kiwon lafiya da dai sauransu a yankunan da bala'in ya rutsa da su."

Ban da ba da kudade da kayayyakin agaji, kasashe da shiyyoyi da yawa sun kuma aika da kungiyoyin agaji da likitoci zuwa yankunan da girigzar kasa ta shafa a kasar Sin. A gun taron kuma, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin, Mr.Qin Gang ya ce, Sin na musu godiya, kuma tana son ci gaba da hada gwiwa da sauran kasashe a fannin yaki da bala'i.(Lubabatu)


1 2