
A ran 5 ga wata, an mika wutar yola ta gasar wasannin Olympics ta Beijing a biranen Xiangtan da Shaoshan da ke tsakiyar kasar Sin, ta hakan ne, aka kammala aikin mika wutar yola na rana ta farko a lardin Hunan cikin nasara.

Da karfe 8 da minta 15 na ran nan da safe, kafin a fara mika wutar yola, dukkan jama'ar da ke wurin sun nuna jimami har tsawon minti daya ga wadanda suka mutu sakamakon girgizar kasa a lardin Sichuan.

Tsawon hanyar da aka mika wutar yola a wannan rana ya kai kilomita 82.1, mutanen da yawansu ya kai 205 sun mika wutar yola a wannan rana. Da hakan ne, aka kammala aikin mika wutar yola na rana ta farko a lardin Hunan cikin nasara.(Danladi)
|