An yi taron kungiyar tsara fasalin aikin sake gina yankunan yawon shakatawa bayan bala'in girgizar kasa na lardin Sichuan a karo na farko a ran 4 ga wata a birnin Chengdu, bisa shirin kudurin da aka yi, an ce, za a kammala aikin sake gina yankunan yawon shakatawa a lardin Sichuan nan da shekaru 3 masu zuwa wato daga shekarar 2008 zuwa shekarar 2010.
Shugaban hukumar yawon shakatawa ta kasar Sin Shao Qiwei ya furta cewa, yankunan da shirin ya shafa su ne yankuna mafi fama da bala'in girgizar kasa kamar gundumar Wenchuan, amma lardunan Shanxi da Gansu za su kula da aikin sake ginawa su da kansu a karkashin tushen shirin sake gina yankin yawon shakatawa na lardin Sichuan. Ya kuma nuna cewa, za a iya bude kofa ga 'yan yawon shakatawa a yankin Zhuhai na kudancin lardin Sichuan da bai samu bala'in girgizar kasa ba da kuma yankin Jiu Zhaigou da bai yi fama da bala'in girgizar kasa mai tsanani ba, amma ba za su bukaci bin wannan shirin ba.(Lami)
|