Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-05 11:01:38    
An fara mika wutar yola ta gasar wasannin Olympic ta Beijing a birnin Xiangtan

cri

Ran 5 ga wata, an fara mika wutar yola ta gasar wasanin motsa jiki ta Olympic ta Beijing a birnin Xiangtan da ke lardin Hunan a tsakiyar kasar Sin.

A wannan rana da karfe 8 da minti 15 da safe, kafin aka fara yin bikin yawo da wuta, mutane da ke wurin sun yi shiru har minti daya don nuna alhini ga 'yan uwammu da suka mutu a cikin girgizar kasa da ta fadawa gundumar Wenchuan a lardin Sichuan.

An fara yin bikin mika wutar yola na zango na Xiangtan a dandalin Dong Fanghong, kuma a karshen dai, za a kai wutar wasannin Olympic zuwa dakin wasannin motsa jiki na jami'ar Xiangtan. Daga bisa kuma bayan hanya mai tsawon kilomita 50, za a kai wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing zuwa birnin Shaoshan watau garin Mao Zedong tsohon shugaban kasar Sin, kuma da karfe 2 da yamma za a fara bikin yawon-yada-kanin-wani wajen mika wutar wasannin Olympic na Beijing a birnin Shaoshan.

A wannan rana, tsawon hanyar mika wutar wasannin Olympic na Beijing zai kai kilomita 82.1, kuma a cikinsu hanya mai tsawon kilomita 21.8 za a yi shi ne da gudu, masu rike da wuta 205 za su shiga cikin wannan bikin.(Bako)