
A cikin 'yan kwanakin nan, ana iya ganin ayyukan sake farfadowa a ko'ina a gundumomi da birane na lardin Sichuan na kasar Sin wadanda suke fama da mummunan bala'in girgizar kasa.
Bisa rahoton da muka samu, an ce, an riga an tsara jadawalin sake farfado da masana'antun lardin Sichuan, wato a cikin tsawon wata guda, kamata ya yi a duba irin barnar da wadannan masana'antu suka samu daga manyan fannoni. A cikin tsawon watanni uku, ya kamata a taimakawa masana'antun wajen sake farfado da ayyukansu daya bayan daya. A cikin tsawon shekara guda kuma, kamata ya yi dukkanin masana'antu wadanda suka gudanar da ayyukan sake farfadowa su kaddamar da ayyukan sake farfadowa daga dukkan fannoni.

Bisa labarin da aka samu daga hedkwatar bada jagoranci ga ayyukan yaki da bala'in girgizar kasa da ceton mutane ta lardin Sichuan, an ce, yanzu haka a biranen Chengdu, da Deyang, da Mianyang, galibin masana'antu wadanda kudin shiga da suka samu a kowace shekara ya kai Yuan miliyan 5 suna gudanar da ayyukan sake farfadowa ba ji ba gani. Yawan masana'antun da suke gudanar da ayyukan sake farfadowa a halin yanzu a birnin Chengdu ya tasam ma kashi 95 daga cikin dari. Kazalika kuma, adadin masana'antun da suke gudanar da ayyukan sake farfadowa a biranen Deyang da Mianyang ya zarce kashi 60 daga cikin dari.(Murtala)
|