Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-05 10:54:53    
Kasashen duniya 166 da kungiyoyin kasa da kasa 16 sun bayar da tallafi ga kasar Sin

cri
Rahoto daga taron manema labaru da ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya jiya 4 ga wata ya ce, bayan da mummunan bala'in girgizar kasa ya fadawa gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin, gaba daya akwai kasashen duniya 166, da kungiyoyin kasa da kasa 16 wadanda suka samar da tallafin kudi ko kayayyakin agaji ga kasar Sin, ciki har da tsabar kudaden da yawansu ya kai kimanin Yuan biliyan 3.555, adadin kayayyakin agaji ya riga ya zarce ton 5000.

A waje daya kuma, kungiyoyin ceton mutane cikin gaggawa daga kasashen Japan, da Rasha, da Koriya ta Kudu, da Singapore sun shiga cikin ayyukan yaki da bala'in girgizar kasa da ceton mutane, akwai kuma kungiyoyin masu aikin jinya 9 daga kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa daban-daban wadanda suka gudanar da ayyukan yiwa mutanen da suka ji rauni jiyya a yankunan da bala'in girgizar kasa ya ritsa da su.

Bangaren Sin da abin ya shafa ya ce, Sin na nuna matukar godiya ga irin gudummowar da gamayyar kasa da kasa suka bayar. Yayin da take kokarin gudanar da ayyukan sake farfadowa bayan bala'in, Sin za ta cigaba da bude kofarta ga kasahen duniya daban-daban, da nuna maraba ga taimako da goyon-baya daga wajensu daidai bisa bukatar yankunan dake fama da mummunan bala'in girgizar kasa.(Murtala)