Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-05 10:50:01    
Akwai nas-nas fiye da 20 daga kabilu daban daban kamar su kabilun Han da Uygur, da kuma Hui da dai sauransu

cri

Suna aiki a cibiyar kula da aikin kashe kwayoyin cuta ta asibitin, aikinsu shi ne samar da duk kayayyakin aiki na asibiti, wadanda aka kashe kwayoyin cuta, sabo da haka ne, ana iya cewa, shi ne wani muhimmin sashe ne na asibitin. Malama Ma Binna, wata 'yar kabilar Hui, ita ce wata nas da ke aiki a cibiyar kula da aikin kashe kwayoyin cuta. A shekarar 1981, Ma Binna ta fara aikinta a wannan cibiya ta asibiti na farko mallakar jami'ar likitanci ta jihar Xinjiang, wato tana aiki a nan har shekaru fiye da 20. Ta gaya wa wakilinmu cewa, "Da farko, babu wanda ke sha'awar yin aiki a wannan ofishi na asibitin, sabo da kullum ana yin aiki da ruwa, da kuma omo, wasu suna ganin cewa, ba a kasancewa da fasaha da kyakkyawar makoma a ofishin. Amma, na yi sha'awar wannan sana'a bayan da na yi aiki cikin wani lokaci. Cibiyar samar da kayayyakin aiki na asibiti, wadanda ake kashe kwayoyin cuta, wani muhimmin sashe ne da ya wajabta ga ko wane asibiti, ingancin ayyukan ofishinmu na saba sosai da ingancin duk ayyukan asibitin."

Ma Binna tana ta tsayawa kan wannan aikin da ake ganin cewa, wai bai kasance da fasaha a cikinsa ba, tana shan wahaloli da yawa wajen aikinta. A lokacin da take fara aiki a ofishin kashe kwayoyin cuta, ta kula da ayyukan kwanke kwalabai, kuma tana ta yin aiki nan har shekaru goma. A cikin wannan lokaci, duk daliban da aka dauko su daga jami'arsu sun bar aikinsu daya bayan daya bisa dalilai daban daban, amma Ma Binna tana ta yi aiki a nan. Ta ce, "A shekaru 80 na karni 19, asibitinmu yana baya sosai wajen na'u'rorin kashe kwayoyin cuta, sabo da haka, wajibi ne mu wanke kayayyakin aiki da hannu. Da sassafe na je aiki, bayan da na gama aikina, rigunan da na sanya dukansu sun jiku cikin ruwa. Lallai na sha wahala sosai a wancan lokaci."

A shekarar 1993, Ma Binna ta zama shugaban nas-nas?kuma ta kara yin fahimta kan aikin kashe kwayoyin cuta. A lokacin da asibitinsu ke shirya gina sabon gini, bisa fasahohin da ta samu, Ma Binna ta gabatar da ra'ayoyinta a jere game da kyautatta shacin gine-gine na cibiyar kashe kwayoyin cuta. A karshe dai, kamannin cibiyar ya sake, bisa sha'awar da ta gabata. Yanzu, kullum shugabanni da sauran masu aikin likitanci na asibitocin da ke wurarre daban daban na jihar Xinjiang suna zuwa asibiti na farko mallakar jami'ar likitanci, don yin ziyara. Ma Binna ta ce, gabatar da fasahohin zamani da ta samu wajen aiki, wannan ne abin farin ciki sosai.

'Yar kabilar Uygur Sahipjamal, wata nas ce da ke aiki a dakin tiyata na asibitin, tana aiki a nan har shekaru 12. Nas-nas na shan aiki sosai a dakin tiyata, sabo da haka, Sahipjamal ta aika da 'danta da shekarun haihuwarsa ya kai 3 kawai zuwa gidan mamarta. Bayan da ta gama aikinta ta koma gida, ta kan buga waya ga 'danta, wannan abu ne mai tsuma jiki da farin ciki gare ta. Ko da ya ke tana shan aiki sosai, amma ba ta taba kokawa ga wannan ba, ta gaya wa wakilinmu cewa, "Da ma mamata ta taba yin aikin nas, kullum tana sanya tufaffi masu launin fari, kuma tana hira tare da masu sami ciwo, har ma a wasu lotuka, iyalan masu sami ciwo da yawa sun zo gidanmu don nuna godiya. A wancan lokaci, jikina ya tsumu sosai, na yi tunanin cewa, zan yi kokari don zama wata nas kamar mamata." Daga baya, Sahipjamal ta je aiki a dakin tiyata, amma aikin nan bai yi kamar abin da ta tuna a da ba, amma tana ganin cewa, tun da ta samu aikin nan, wajibi ne ta yi kokari sosai kan aikin. Yanzu, tana son aikinta sosai.

Ko da ya ke aikin nas ya yi kamar cikin sauki, amma wannan aikin da a kan maimaita sau da yawa a ko wace rana yana bukatar nas-nas masu daukar hakki bisa wuyansu, da kaunar mutane.

A ko wace rana, 'yar kabilar Uygur Patigul da ke aikin nas a dakin asibitin da ke kula da jarirai, ta kan auna yawan zafi, da yin allura, da kuma yin wanke-wanke ga jariran da aka haife su ba da dadewa ba. Tun daga watan Oktobba na shekarar 1987 har zuwa yanzu, Patigul tana ta yin aikin nas a sashen haihuwa kusan shekaru 20. Da farko, Patigul ba ta fahimci sana'ar ba, kuma ba ta san wane irin aiki ne da za ta yi nan gaba ba. Ya zuwa lokacin da take yin gwajin aiki a wannan asibiti, ta fahimci sana'ar nas a hakika. Ta ce, "A lokacin da nake fara aikina, sabo da ina kaunar yara sosai, don haka na yi fatan yin aiki a sashen haihuwa. Na kan ba da ilmin kula da jarirai ga sabbin mama, ina jin farin ciki wajen aikina."

Amma, a wasu lokatai, Patigul ba ta iya kula da yaranta sosai ba. Sabo da kullum tana aikin dare, don haka ba ta da isasshen lokaci don koyar da yaranta.