Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya bayar an ce, babbar kungiyar Red Cross ta Sin ta ware kudin jin kai da yawansu ya kai Yuan miliyan 500 wajen sake gina makarantu da gidajen kwana a wuraren da bala'in girgizar kasa ta shafa.
Wani jami'in babbar kungiyar ya bayyana cewa, a yanzu haka dai, ana gaggauta tsara shirin sake raya lardin Sichuan bayan bala'in. Wa'adin farfado da wanann lardi shi ne shekaru takwas. ( Sani Wang)
|