Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya bayar an ce, zaunannen taron majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta amince da ' Daftari shirye-shirye kan sake gina yankin Wenchuan bayan bala'in girgizar kasa' bisa ka'ida. An gudanar da wannan taro ne yau Laraba a nan birnin Beijing.
Firaminista Wen Jiabao ya shugabanci taron, wanda ya yi nuni da cewa, ya zama wajibi a kaddamar da wannan daftarin shirye-shirye, wanda ya dora ayyukan farfadowa da sake gina yankin Wenchuan cikin dokokin shari'a. A fili ne daftarin ya tabbatar da manufofi da ka'idojin da abun ya shafa a kan cewa a mayar da mutane a gaban komai, da tsara shirye-shirye ta fuskar kimiyya, da daidaita harkoki ta tsararriyar hanya kuma cikin mataki-mataki; Sa'annan taron ya nemi da a yi bayani ba tare da rufa-rufa ba kan yadda ake rarrabawa da kuma yin amfani da kudin agaji da kayayyaki da kuma gidajen kwana na wucin gadi; Dadin dadawa, taron ya bukaci da a dora muhimmanci kan farfado da zirga-zirga, da sadarwa, da samar da wutar lantarki da ruwan sha, da sake gina gidajen kwana da makarantu da kuma asibitoci yayin da ake gudanar da ayyukan farfadowar yankin. ( Sani Wang )
|