A kwanan baya, ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar Sin ta bayar da babbar ka'idar tsugunar da marayu da tsoffi da nakasassu da dukkan iyalansu suka mutu a cikin bala'in girgizar kasa da ya auku a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan.
Game da yaran da har yanzu ba a dauke su ba tukuna, bisa ka'idar da aka bayar, an ce, da farko dai a yi namijin kokarin neman iyayensu da iyalansu. Sannan kuma a tsugunar da su a cikin gidajen jin kai da makarantun gwamnati da suke da sharuda masu kyau. Idan akwai matsalar tsugunar da su a lardin Sichuan, ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar Sin za ta daidaita aikin tsugunar da su. Bayan da aka tabbatar da asalin marayu, za a dauki hanyoyi iri daban daban na tsugunar da su. Musamman ne an nuna cewa, lokacin da ake tsugunar da marayun da suka kai fiye da shekaru 10 da haihuwa a sauran gidaje, dole ne a nemi amincewa daga marayu. (Sanusi Chen)
|