Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-04 15:18:09    
An kammala aikin mika wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing a birnin Changsha

cri

Yau wato ran 4 ga wata, an kammala aikin mika wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing a birnin Changsha na lardin Hunan da ke kudancin kasar Sin.

A misalin karfe 8 da minti 12 da safe, a matsayinsa na mai rike da wutar yola na farko na zangon Changsha, Xiong Ni, shahararren tauraron wasanni na kasar Sin da ya taba zama zakara a cikin gasar tsinduma cikin ruwa daga kan dandamali ta wasannin Olympics na Sydney ya tashi daga rumfar Aiwan da ke wurin shan iska na dutsen Yuelushan, ta haka an kaddamar da aikin mika wutar na yau. Bayan mika wutar a tsakanin masu rike da wutar yola 206, a karshe dai wutar ta isa cibiyar wasanni ta Helong. Aikin ya shafi awoyi fiye da 3, kuma tsawon hanyar mikawa ya kai kilomita 20.8.

Kafin a kaddamar da aikin mika wutar, dukkan mutanen da suka sa hannu a cikin aikin sun tsaya cik sun yi shiru har minti guda domin nuna ta'aziyya ga mutanen da suka mutu sakamakon mummunar girgizar kasa da ta auku a gundumar Wenchuan.(Kande Gao)