Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-04 15:15:26    
Rashin jin dadin aure zai kawo cutar bugun jini

cri

Bisa wani sabon binciken da manazarta na kasar Amurka suka gudanar, an ce, kullum mutane da ke jin dadin aure su kan iya kiyaye bugun jininsu kamar yadda ya kamata, kuma game da mutanen da ba su kulla kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin namiji da mata, ba su da lafiyar bugun jini, har ma ba su fi wadanda ba su yi aure ba kyau.

Julianne Hoult, wata kwararriya a fannin ilmin tunanin dan Adam ta jami'ar Brigham Young ta kasar Amurka ta ba da rahoto a kan 'jaridar shekara-shekara ta ilmin likitanci kan tafiyar da harkoki', cewa an zabi mutane 204 da suka yi aure da kuma mutane 99 da ba su yi aure ba tukuna wajen dauke da na'urorin rubuta karfin bugun jini, ban da wannan kuma an bukaci mutane maza da mata da suka yi aure da su amsa tambayoyin da aka yi musu wajen ingancin aurensu.

Daga baya kuma binciken ya gano cewa, idan mutane sun nuna gamsuwa ga aurensu, to za su samu bugun jini kamar yadda ya kamata. Haka kuma game da mutanen da ba su nuna gamsuwa ga aurensu ba, kullum karfin bugun jininsu ya fi yawa, har ma matsaikacin karfin bugun jininsu ya fi wadanda ba su yi aure ba yawa. Amma kafin wannan ana ganin cewa, mutanen da suka yi aure sun fi samun lafiyar jiki idan an kwatanta su da wadanda ba su yi aure ba.

Karen Matthews, kwararre a fannin cututtuka masu yaduwa na jami'ar Pittsburgh ta kasar Amurka ya bayyana cewa, ya kamata a mai da hankali a kan wannan bincike, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da a da mutane ba su lura da tasirin da ingancin aure ya bai wa bugun jini ba.

To, masu sauraro, yanzu sai ku shakata kadan, daga baya kuma za mu yi muku wani bayani daban kan cewa, karfin bugun jini yana da nasaba da dabi'ar cin abinci.

Ba kawai ingancin aure yana iya ba da tasiri ga karfin bugun jini ba, har ma dabi'ar cin abinci yana da nasaba da karfin bugun jini.

Bisa labarin da wata tashar Internet ta kasar Birtaniya ta bayar a ran 21 ga wata, an ce, manazarta na jami'ar Imperial ta kasar Birtaniya da jami'ar Northwestern ta kasar Amurka da dai sauran hukumomi sun yi nazari kan dangantakar da ke tsakanin karfin bugun jini da abinci bisa wasu sinadari da jikin dan Adam ke samarwa sakamakon sauye-sauyen halittu.

Manazarta sun gudanar da wannan bincike ga mutane 4630 masu matsakaitan shekaru da haihuwa da suka zo daga kasashen Birtaniya da Amurka da Sin da kuma Japan. Kuma sakamakon ya bayyana cewa, baligai na Birtaniya da Amurka suna iya samar da sinadarin sauye-sauyen halittu kusan iri daya, haka kuma halin da suke ciki wajen kamuwa da cutar bugun jini ya yi kusan iri daya. Amma ko da yake Sinawa da Japanawa suna da kwayoyin halitta kusan iri daya, amma sun sha bamban a fannin sinadarin sauye-sauyen halittu. Japanawa da suke zama a kasar Amurka suna iya samar da sinadarin sauye-sauyen halittu na salon Amurka, kuma wannan ya shaida cewa, hanyar zaman rayuwa musamman ma dabi'ar cin abinci tana iya taka muhimmiyar rawa a wannan fanni.

Ban da wannan kuma manazarta sun bayyana cewa, wannan hanyar nazari ta ba da jagoranci wajen kara fahimtar abincin da za su haddasa cutar bugun jini, da kuma samar da wata sabuwar dabara mai kyau wajen rigakafin hauhawar jini.(Kande Gao)