Wakilinmu ya samu labari daga ma'aikatar zirga-zirga ta kasar Sin cewa, ya zuwa ran 2 ga wata, a cikin kauyuka da garuruwa 439 da suka fi fama da bala'in girgizar kasa na lardin Sichuan, an samu farfado da hanyoyi 424, wadanda suka dauki kashi 97 cikin dari na dukkan hanyoyin wurin.
Kyakyawan halin da hanyoyi ke ciki ya ba da tabbaci ga jigilar kayayyakin agaji zuwa yankuna mafi fama da bala'in. Daga ran 12 ga watan Mayu zuwa ran 1 ga watan Yuni, yawan kayyayakin agaji da aka yi sufurinsu ta hanyar mota a lardunan Shanxi da Gansu da Sichuan da kuma birnin Chongqing ya kai fiye da ton miliyan 3.
Bugu da kari kuma, hanya maras shinge a kan ruwa dake madatsar ruwa ta Sanxia ta taka muhimmiyar rawa sosai. Tun daga ran 14 ga watan Mayu da hukumar kula da aikin sufuri na Sanxia ta fara yin amfani da hanya maras shinge a kan ruwa zuwa ran 1 ga watan Yuni, yawan kayayyakin agaji da jiragen ruwan Kogin Yangtse da suka yi sufuri a kan hanyar ruwa ta madatsar ruwa ta Sanxia ya kai ton dubu 156.(Lami)
|