Ran 3 ga wata, manema labaru sun sami labari daga ma'aikatar ilmi ta kasar Sin cewa, hukumomin ba da ilmi na matakai daban daban na kasar Sin suna daukar matakai cikin himma wajen karbar daliban da bala'in girgizar kasa ya ritsa da su da suka zo wurinsu don yin karatu.
Bisa kididdigar da aka samu, an ce, ya zuwa yanzu larduna da birane biyar watau ChongQing da Jiangsu da Guangxi da Anhui da Shandong sun karbi dalibai fiye da 5100.
A matsayinsa na wani lardi da ya fi shan wahalar bala'in girgizar kasa, lardin Sichuan yana gaggauta gina makarantun tanti da kara daukar dalibai na firamare da na sakandare, don sanya wa daliban da girgizar kasa ta ritsa da su, su sake komawa makarantu domin yin karatu. Jami'o'I na lardin Sichuan sun kafa "makarantun samar da kauna" da "makarantun samar da kauna ga kowa". Ya zuwa ran 26 ga watan Mayu, jami'o'in lardin Sichuan sun karbi 'yan makarantun da suka daga yankunan fama da bala'in girgizar kasa da yawansu ya kai dubu 28.(Bako)
|