Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-04 14:06:35    
Kasashen duniya suna ci gaba da samar da taimako ga yankunan da ke fama da girgizar kasa na kasar Sin

cri
A 'yan kwanakin nan da suka gabata, kasashen duniya suna ci gaba da samar da kudade da kayayyakin taimako ga yankunan da ke fama da girgizar kasa na lardin Sichuan na kasar Sin.

Gwamnatin hadaddiyar daular Larabawa ta samar da kudade dala miliyan 50 ga bangaren Sin. Kuma kayayyakin taimako na sabon rukuni da nauyinsu ya kai ton 60 da kasar Rasha ta samar sun isa birnin Chengdu a ran 3 ga wata, wadanda darajarsu ta zarce kudin Sin wato Yuan miliyan 6. Haka kuma a ran 3 ga wata, jiragen sama na soja na kasar Jamus da ke dauke da tantuna na rukunin farko sun tashi daga Jamus, kuma an kiyasta cewa za su isa birnin Chengdu a ran 4 ga wata.

Ban da wannan kuma gwamnatin kasar Monaco ta tsai da kudurin samar da kudaden taimako EURO dubu 100 ga bangaren Sin ta kungiyar kiwon lafiya ta duniya wato WHO.

Bugu da kari kuma gwamnatocin wurare na kasar Pakistan sun sake samar da kudade dala dubu 170 da kuma tantuna 1000 ga bangaren Sin bisa tushen samar da tantuna 500.(Kande Gao)