Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-04 12:30:32    
Beijing tana rubanya kokari domin tabbatar da tsaron lafiyar al'umma a lokacin gudanar da gasar wasannin Olympic

cri
Kowa ya sani cewa, za a yi gasar wasannin Olympic a karo na 29 a nan Beijing a ran 8 ga watan Agusta a wannan shekara. Batun tsaron lafiyar al'umma a lokacin gudanar da gasar waasnnin Olympic yana ta jawo hankulan rukunoni daban daban na zaman al'ummar kasa sosai. Ya zuwa yanzu dai Beijing ta riga ta fito da tsarin magance bullowar matsalolin tsaron lafiyar al'umma da ya hada da jerin shirye-shiryen ko-ta kwana. Sa'an nan kuma, ta kafa tashoshin taimakon gaggawa a kauyen wasannin Olympic da filaye da dakunan wasa da sauran gine-ginen da abin ya shafa, ta kuma samar da isassun injunan kiwon lafiya da likitoci. Ban da wannan kuma, ta inganta sa ido kan ingancin abinci da ruwan sha da hanyoyin yaduwar cututtuka masu yaduwa da halittun da suke yada cututtuka masu yaduwa da kuma iska mai guba ta nukiliya a duk fadin birnin.

A makon da ya gabata, a nan Beijing, Jin Dapeng, shugaban sashen ba da tabbaci ta fuskar kiwon lafiya na kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing ya bayyana cewa, a lokacin da ake gudanar da gasar wasannin Olympic, kwamitin zai tabbatar da ganin cewa, ba za a sami bullowar munanan cututtuka masu yaduwa a Beijing ba, kuma cikin lokaci ne za a shawo kan cututtuka masu yaduwa da aka shigo da su. Ban da wannan kuma, za a tabbatar da rashin kasancewar guba cikin abinci da gurbata ruwan sha. Za a daidaita al'amuran ba zata da za su kawo barazana ga tsaron lafiyar al'umma da hare-haren ta'addanci cikin lokaci. Za a tabbatar da yin jiyya mai inganci ga ko wane majiyyaci nan take yadda ya kamata kuma cikin lokaci da kuma kiwon lafiyarsa. Mr. Jin ya ce,'Yanzu hukumar Beijing ta kafa tsarin ko-ta-kwana na ba da jagoranci ga ayyukan tsaron lafiyar al'umma, haka kuma, ta riga ta fito da tsarin shirye-shiryen ko-ta-kwana na tsaron lafiyar al'umma, sa'an nan kuma, Beijing ta kyautata karfinta sosai a harkokin kiwon lafiya a lokacin gudanar da gasar wasannin Olympic.'

Yin rigakafi da shawo kan cututtuka masu yaduwa na matsayin wasani muhimmin bangare na tabbatar da tsaron lafiyar al'umma. Yanzu sashen ba da tabbacin kiwon lafiya na kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing ya riga ya yi hadin gwiwa da hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO da birnin Tianjin da lardunan Hebei da Shanxi da Liaoning da Jilin da jihar Mongolia ta Gida da ke makwabtaka da shi, sun kafa tsarin yin rigakafi da shawo kan munanan cututtuka masu yaduwa cikin hadin gwiwa. Zhao Tao, shugaban sashen yin rigakafi da shawo kan cututtuka masu yaduwa na hukumar kiwon lafiya ta Beijing ya yi karin bayani da cewa,'Tun daga shekarar 2006, mun soma yin kimantawa kan barazanar da wasu cututtuka masu yaduwa da su kan bullo a Beijing suka kawo, ciki, har da wasu cututtuka masu yaduwa ta hanyar numfashi, kamar mura mai kamuwa. A lokacin gudanar da gasar wasannin Olympic, 'yan wasa da masu yawon shakatawa da suka zo daga sauran kasashe za su zo Beijing, shi ya sa muka yi kimantawa kan barazanar da wasu cututtuka masu yaduwa da aka shigo da su, kuma ba safai su kan bullo a kasarmu ko kuma birninmu ba.'

Mr. Zhao ya ambaci cewa, lokacin zafi ya yi ne a daidai lokacin da ake gudanar da gasar wasannin Olympic ta Beijing, shi ya sa tilas ne a kara dora muhimmanci kan wasu cututtuka masu yaduwa da ake kamuwa da su daga abinci da kuma ta hanyoyin hanji. Yanzu Beijing ta kafa ingantaccen tsarin sa ido kan ingancin abinci, kuma dukkan hukumomin kiwon lafiya na birnin sun iya gabatar da rahoto kan barkewar cututtuka masu yaduwa ta hanyar internet, don haka za a iya yin rigakafi da sa ido kan bullowar cututtuka mas kamuwa da ake kamuwa da su daga abinci. Ban da wannan kuma, hukumar kiwon lafiya ta Beijing ta kafa tsarin binciken alamun cututtuka masu yaduwa a muhimmin yanki na wasannin Olympic, za ta sa ido a tsanake kan alamu 5 da mutane za su nuna, wato yin zafi da zawo da kuraje a fata da jan ido da kuma ta jika.

Baya ga yin rigakafin cututtuka masu yaduwa, kashe halittun da suka yada cututtuka masu yaduwa yana da muhimmanci sosai wajen tabbatar da tsaron lafiyar al'umma. Hukumomin da abin ya shafa sun riga sun tsara shirin kashe halittun da suka yada cututtuka masu yaduwa, sun kuma kashe irin wadannan halittu sau 2 a duk fadin Beijing. Liu Zejun, darektan kwamitin aikin tsabta na Beijing ya yi karin bayani da cewa, a ran 20 ga wata, za a sake kashe irin wadannan halittu a Beijing. Mr. Liu ya ce,'A lokacin da ake gudanar da gasar wasannin Olympic, za a tabbatar da ma'aunin kasar Sin a aikin tsabta a wuraren da ke zagaye filaye da dakunan wasa har kilomita 2. Haka kuma, za a kshe dukkan sauro da kuda da kuma beraye a cikin dukkan filaye da dakunan wasa.'

Kazalika kuma, Mr. Jin ya gaya wa wakilinmu cewa, domin tinkarar batutuwan ba zata da za su kawo barazana ga lafiyar al'umma, kuma mai yiwuwa za su barke a lokacin gudanar da gasar wasannin Olympic. Hukumar Beijing ta riga ta share fage sosai. Saboda haka, a lokacin da ake gudanar da gasar wasannin Olympic a nan Beijing, za a tabbatar da tsaron lafiyar al'umma kamar yadda ya kamata.(Tasallah)