|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2008-06-03 11:17:17
|
 |
'Yan kallo na kasashen ketare ba za su iya samun iznin shiga kasar Sin ba ta hanyar sayen tikitin gasar wasannin Olympic
cri
'Yan kallo na kasashen ketare ba za su iya samun iznin shiga kasar Sin ba ta hanyar sayen tikitin gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta Beijing, ya kamata su bi dokokin kasar Sin da aka tsaida musu, su je ofishin jakadancin Sin dake kasashen waje don neman iznin shiga kasar Sin.
Ran 2 ga wata, tashar internet ta gasar wasannin Olympic ta Beijing ta bayar da wannan labari. A wannan rana kuma, tashar internet ta bayar da "takaitaccen bayyani a kan dokokin kasar Sin game da mutanen kasashen waje su shiga ko fita daga kasar Sin a lokacin gasar wasannin Olympic ta kasar Sin da kuma yada zango a kasar Sin a wancan lokaci", abubuwan da suke ciki sun shafi shiga da kuma fita daga kasar Sin da kallon wasanni da yawon shakatawa da samun wuraren kwana da zirga-zirgar kasar da abinci da abubuwan sha da abubuwan ban nishadi a wannan kasar don bayar da dokoki da ka'idojin kasar Sin ga 'yan wasannin kasashen waje da jami'an gwamnati da manema labaru na kafofin yada labaru wadanda za su shiga kasar Sin a lokacin gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta Beijing.(Bako)
|
|
|