Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-03 10:40:17    
Mr. Li Changchun ya kai ziyara ga wuraren da ke fama da bala'i na lardin Sichuan

cri

Ran 3 ga wata da safe, Mr. Li Changchun memban zaunanen kwamiti na ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin ya kai ziyara ga birnin Dujiangyan doumin ganin halin da gidan ibada na sarkuna biyu da sauran kayayyakin tarihi ke ciki.

Bisa burin da Mr. Hu Jintao babban sakatare na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin ya yi, tun daga ran 1 ga wata, Mr. Li Changchun ya kai ziyara ta musamman ga wuraren da ke fama da bala'in girgizar kasa na lardin Sichuan domin gai da jama'a da jami'ai da ke fama da bala'i da mutunen ayyukan ceto, haka kuma ya yi rangadin ayyukan fama da bala'i.

A cikin kwanakin baya, bi da bi ne Mr. Li Changchun ya yi rangadi ga biranen Mianyang, da Pingwu, da Deyang. Ya nuna cewa, dole ne jam'iyyar kwaminis ta Sin da gwamnatin kasar Sin za su ba da taimako ga mutanen da ke fama da bala'i wajen sake gina gidaje.

Mr. Li Changchun ya bukaci jami'an da ke wurin su yi kokari domin kwantar da hankalin iyalai na mutanen da suka mutu da mutanen da suka jikkata.