
Yayin da kakakin ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin, Mr.Mao Qun'an ke hira da wakilin tashar internet ta gwamnatin kasar Sin a yau 2 ga wata a nan birnin Beijing, ya bayyana cewa, yanzu ma'aikata 16,112 ne ke gudanar da ayyukan kiwon lafiyar jama'a da rigakafin cututtuka masu yaduwa a yankunan da girgizar kasa ta shafa, kuma sun gudanar da aikin musamman na kashe kwayoyin cuta don tabbatar da rashin samun annoba bayan bala'in.
Mr.Mao Qun'an ya ce, ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin ta sanya ma'aikatan kiwon lafiya a kowace gunduma da gari da kauye da girgizar kasar ta shafa, kuma ta tabbatar da yawansu ya kai daya zuwa uku a cikin kowane kauye. Bayan haka, ta tura masana ko kwararru a fannin rigakafin cututtuka zuwa gundumomi da garuruwa daban daban, don su ba da jagoranci a kan ayyukan rigakafin cututtuka.

Mr.Mao Qunan ya kuma jaddada cewa, ingancin ruwan sha na da muhiammanci sosai wajen rigakafin annoba bayan bala'i. A lokacin da ake rigakafin cututtuka masu yaduwa a yankunan da girgizar kasa ta shafa, ba ma kawai za a sa ido a kan ruwan sha da ake samarwa ga jama'a ba, haka kuma za a sanya ido a kan wasu mafaran ruwa, don tabbatar da ingancin ruwan sha.(Lubabatu)
|