|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2008-06-02 20:52:52
|
Kasashen duniya sun cigaba da nuna juyayi da bayar da taimako ga kasar Sin kan sakamakon girgizar kasa
cri
Kwanan baya, kasashen duniya sun cigaba da nuna juyayi da bayar da gudumowa ga kasar Sin, a sakamakon girgizar kasa da aka samu a lardin Sichuan na kasar.
Firayin ministan kasar Tunisiya Mohamed Ghannouchi, da shugaban majalisar ba da shawara ta kasar Saudi Arabia Saleh Abdullah, da shugaban majalisar dokoki ta kasar Iraqi Mahamud Al Mashhadani, da shugaban majalisar dokoki ta kasar Georgia Nino Burdzanadze, da kuma shugaban majalisar dattijai ta kasar Barbados Branford Taitt, sun nuna juyayi ga kasar Sin daya bayan daya.
Bugu da kari kuma, gwamnatoci, da kungiyoyi daga kasashen Laos, da Pakistan, da Isra'ila, da Katar, da Ukraine, da Georgia, da Spain, da kuma Amurka sun bayar da taimakon kudi, ko kayayyakin ceto ga kasar Sin. (Bilkisu)
|
|
|