Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, bayan aukuwar mummunan bala'in girgizar kasa a ran 12 ga watan jiya a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin, bangarori daban-daban na ciki da kuma wajen kasar suna alla-allar bada kudin karo-karo da kayayyaki ga wuraren da bala'in ya shafa. Ya zuwa jiya Lahadi da misalin karfe 12, duk kasar ta samu kudin karo-karo da kayayyaki, wadanda darajarsu ta wuce kudin Sin wato RMB Yuan biliyan 41 da miliyan 500 daga bangarori daban-daban na ciki da kuma wajen kasar. Sassan da abin ya shafa na kasar Sin da suka karbi wadannan kudin karo-karo da kayayyaki sun tabbatar da cewa, za su bayyana adadin kudin karo-karo da kayayyaki a kan tashoshin internet na kowanensu ba tare da bata lokaci ba yayin da suke rokon sassan binciken kudi kan bincika yadda ake karbar wadannan kudin karo-karo da kayayyaki da kuma yin amfani da su da rarraba su.
Jiya Litinin, ma'aikatar kula da harkokin al'umma ta kasar Sin ta kaddamar da ' Dabarun bayyana bayanai a fili kan yadda ake kulawa da yin amfani da kudade da kayayyaki da ake samarwa domin yaki da bala'in girgizar kasa da bada agaji a yankin Wenchuan'. Shugaban sashen kula da ayyukan bada agaji na ma'aikatar kula da harkokin al'umma ta kasar Sin Mr. Pang Chen-min ya bayyana cewa : ' Yawancin kudin karo-karo da kayayyaki da ma'aikatar din ta samu, ana yin amfani da su ne wajen yin ceto cikin gaggawa, da kwashe jama'ar da bala'in ya galabaitar da su da kuma tsugunar da su ; da warware wahalhalun rayuwa da jama'ar da bala'in ya shafa suke sha a fannin kayan tufafi, da abinci, da kwana da kuma samun jinya da dai sauransu ; da taimaka wa jama'ar da bala'in ya galabaitar da su wajen sake gidajensu da gine-ginen jama'a wadanda suka lalace sakamakon bala'in girgizar kasar'.
A wata sabuwa kuma an ce, kawo jiya dai, kungiyar agaji ta Red Cross ta kasar Sin ta karbi kudin karo-karo da kayayyaki da darajarsu ta dara RMB Yuan biliyan 10. Mataimakin kungiyar din Madam Jiang Yiman ta furta cewa : ' Kungiyar agaji ta Red Cross ta kasar Sin tana daukar matakai don bayyana bayanai ba tare da rufa-rufa ba kan makudan kudade da kayayyaki da ta samu.'
A yanzu haka dai, sashen bincika kudi na kasar Sin ya rigaya ya shiga cikin ma'aikatar kula da harkokin al'umma ta kasar domin binciken yadda ake yin amfani da kudin karo-karo da kayayyaki. Shugaban sashen Mr. Wang Zhongxing ya fada wa wakilinmu cewa: "Za mu dora muhimmanci kan kaddamar da dokoki da ka'idoji da ya kamata kowane sashen kulawa da kuma yin amfani da kayan agaji da ake samar wa wuraren da bala'in girgizar kasa ya shafa; Ban da wannan kuma za mu sa ido kan yadda ake rarraba wadannan kayayyaki bisa doka, ta yadda za a mika su cikin hannun mutane masu shan masifar bala'in da gaske". ( Sani Wang )
|