Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-02 16:37:09    
An riga an kai mutanen da suka ji rauni sama da dubu 10 a yankunan da bala'in girgizar kasa ya ritsa da su na lardin Sichuan zuwa wurare daban-daban na kasar Sin don yi musu jinya

cri
Zuwa ranar 31 ga watan da ya shude, an riga an kai mutanen da suka ji rauni da yawansu ya zarce dubu 10 a yankunan da bala'in girgizar kasa ya galabaitar da su na lardin Sichuan zuwa larduna, da jihohi masu zaman kansu, da biranen dake karkashin shugabancin gwamnatin tsakiya kai-tsaye guda 20, don yi musu jinya.

Yayin da kakakin ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin Mao Qun'an ke zantawa da tashar Internet ta gwamnatin kasar Sin yau 2 ga wata, ya bayyana cewar, domin sassauta matsin-lambar lardin Sichuan wajen ceton wadanda suka ji raunuka ko yi musu jinya, daga ranar 17 ga watan Mayu har zuwa ranar karshe ga watan Mayu, ta hanyar jiragen kasa na musamman guda 21, da jiragen saman musamman guda 99, tare kuma da sauran motoci masu aikin jinya sama da dubu 10 ne, masu aikin jinya sama da dubu 5 sun yi jigilar mutanen da suka ji rauni zuwa asibitoci fiye da 340 na wurare daban-daban na kasar Sin.

Kakaki Mao ya ce, yin jigilar mutanen da suka ji rauni ya samar da kyakkyawan sharadi wajen kyautata sharadin warkar da mutanen da suka ji rauni, da kiyaye lafiyarsu, da sassauta lambar da aka matsawa lardin Sichuan wajen ceton mutane, da daukaka cigaban ayyukan sake farfadowa.(Murtala)