Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-02 16:00:51    
Hu Jintao ya yi rangadin aikinsa a lardin Gansu a kasar Sin don ganin halin da ake ciki wajen yaki da bala'in girgizar kasa da ceton mutane da farfado da wuraren da bala'in ya shafa

cri

Bayan da Hu Jintao ya kawo karshen rangadin aikinsa a yankunan da aka samu bala'in girgizar kasa a lardin ShanXi wanda ke kusa da lardin Sichuan a kasar Sin, ran 1 ga watan Yuni, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya je birnin Longnan da ke lardin Gansu a kasar Sin, don yin shawarwari da mutane da jami'in gwamnati wajen farfado da wuraren da bala'in girgizar kasa ta shafa.

Birnin Longnan da ke lardin Gansu a kasar Sin shi ne wani yankin da ke kusa da gundumar Wenchuan na lardin Sichuan watau wuri ne da aka fi shan wahalar bala'in girgizar kasa.

Hu Jintao ya zo cikin wani jeep, ana shan wahalar tafiya, ya yi rangadin aikinsa a yankunan da aka fi samun mummunan bala'in girgizar kasa. Hu Jintao ya gaya wa jami'in gwamnatin wurin cewa, yayin da ake yin aikin farfado da wuraren da girgizar kasa ta shafa, ya kamata a tsara fasali mai kyau, don inganta kwarewar gidajensu wajen maganin girgizar kasa, haka kuma a warware batun samar da ruwa ga mutanen a kauyuka.

Hu Jintao ya baiwa jama'ar da ke yankunan bala'in girgizar kasa kwarin gwiwa cewa ya kamata su gudanar da aikin kawo albarka da sake farfado da wurare da bala'in ya shafa dogara ga kansu. Haka kuma ya nuna jejeto ga sojojin 'yantar da jama'a da 'yan sanda wadanda ke yaki da bala'in girgizar kasa a wurin.

Hu Jintao ya zo wani asibitin tanti na asibitin jama'a na farko na birnin Longnan, don ganin wadanda suka raunata da masu aikin jinya. Haka kuma ya je ganewa idonsa ayarin ba da aikin jinya na duniya na kasar Pakistan wanda ke taimaka wa kasar Sin wajen ba da jiyya ga masu jin rauni. A madadin gwamnatin kasar Sin da jama'arta, Hu jintao ya nuna godiyarsa ga wadanan mutane.

A wannan rana da dare, Hu Jintao ya kira wani taro a jirgin kasa. Ya yi nuni da cewa, ya kamata a tsaida manufofin musamman wajen farfado da aikin kawo albarka, don rage yawan tasirin da bala'in girgizar kasar ya baiwa tattalin arzikin kasar. Haka kuma dole ne a karfafa zuciyar mutane daga dukkan fannoni, a yi kokari wajen kammala aikin farfado da wuraren da bala'in ya shafa.(Bako)