
Yau ran 2 ga wata da misalin karfe 8 da safe, an fara aikin mika wutar yola ta wasannin Olympic na Beijing a birnin Jingzhou na lardin Hubei na kasar Sin. Shahararren 'dan wasan motsa jiki na kasar Sin kuma zakaran wasan Olympic Zheng Lihui ya zama mai mika wutar yola na farko.

Yau da safe, an iya ganin gajimare a sama, kuma ba zafi kuma ba sanyi a birnin Jingzhou, haka ya dace da yin aikin mika wutar yola. Da karfe 7 da safe, akwai 'yan birnin da dama da suka tattara a filin Jingfeng inda za a fara mika wutar yola don taya murnar aikin mika wutar yola. Kafin a fara wannan aiki, dukkan mutanen dake wurin sun nuna ta'aziyya ga mutanen da suka rasa rayukansu a bala'in girgizar kasa na gundumar Wenchuan har minti daya.

Tsawon hanyar mika wutar yola a birnin Jingzhou ya kai kilomita 18.6, masu mika wutar 208 za su shiga cikin wannan aiki.(Lami)
|