Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-02 15:28:16    
Masana'antun dake fama da bala'in girgizar kasa a lardin Sichuan sun soma farfadowa

cri
Yanzu haka a lardin Sichuan na kasar Sin, masana'antun dake fama da mummunan bala'in girgizar kasa sun riga sun soma ayyukan sake farfadowa daya bayan daya.

Bisa kididdigar da aka yi, an ce, akwai masana'antu sama da dubu 20 wadanda suke fama da mummunan bala'in girgizar kasa. Yawan hasarar kudi da aka samu kai-tsaye ya kai kudin Sin Yuan biliyan 67.

A halin yanzu, masana'antu da dama sun riga sun fara ayyukan sake farfadowa. Zuwa ranar 27 ga watan da ya shude, dukkan masana'antun Sichuan sun riga sun bude kofarsu. Yayin da ake samun barkewar kananan girgizar kasa ta bi-baya, wasu masana'antu sun kammala ayyukansu na gaggyara na'urori da dakunansu, da kiyaye muhimman ababen biyan bukatun jama'a ba tare da matsala ba. Kmafanin DEC wanda ke fama da bala'in girgizar kasa mafi muni ya riga ya fara gudanar da ayyukansa daga dukkan fannoni, kuma ya sa hannu tare da masana'antun samar da wutar lantarki da dama na kasar Sin kan kwangiloli daban-daban da darajarsu ta zarce Yuan biliyan 6 gaba daya.

Kwanan baya, ma'aikatar kudin kasar Sin, da babbar hukumar kula da harkokin haraji ta kasar sun bayar da wata sanarwa kan tabbatar da harkokin sake farfadowa da buga haraji biyo bayan mummunan bala'in girgizar kasa. A waje daya kuma, babbar hukumar masana'antu da kasuwanci ta bullo da manufofi guda 12, a wani yunkurin goyon-bayan yankunan da bala'in girgizar kasa ya ritsa da su wajen sake farfadowa, da gudanar da harkokin kasuwanci yadda ya kamata. Dukkan wadannan matakai za su samar da wani kyakkyawan yanayi wajen sake farfado da masana'antun dake fama da bala'in girgizar kasa.(Murtala)