Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-02 15:27:51    
An kammala gasannin "good luck Beijing" cikin nasara

cri

An kammala gasar iyo ta Marathon ta jerin wasannin "good luck Beijing" da aka yi don zaben 'yan wasannin da za su shiga cikin wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008 a ran 1 ga wata a lambun yawon shakatawa a kan ruwa na Olympic dake unguwar Shunyi ta birnin Beijing, 'yan wasa 22 sun sami damar shiga cikin gasar wasannin Olympic ta Beijing. Daga nan ne, aka kawo karshen jerin gasannin "good luck Beijing" cikin nasara.

An yi jerin gasannin zaben 'yan wasan da za su shiga cikin wasannin Olympic, da dudduba filaye da dakunan yin gasanni da kungiyoyin 'yan takara da aikin sufuri da sauran ayyuka kafin a yi gasar wasannin Olympic tushe ne na yin wasannin Olympic cikin nasara. Tun daga watan Yuli na shekarar 2007, kwamitin wasannin Olympic na Beijing ya yi gasannin "good luck Beijing" har sau 42, domin yin wasannin share fage ga wasannin Olympic na Beijing.

A watan Janairu da watan Mayu na shekarar 2008, cibiyar yin wasan iyo da filin wasa na kasar Sin sun bude kofa daya bayan daya, an yi gasar iyo da wasan guje-guje da tsalle-tsalle a ciki, dakunan yin wasanni da hidimomin da aka bayar sun sami babban yabo sosai.

Mataimakin shugaban zartaswa na kwamitin wasannin Olympic na Beijing Yang Shuan ya furta a kwanakin baya cewa, bayan yin wasannin "good luck Beijing" a filaye da dakunan yin wasanni, an tabbatar da cewa, manyan ayyuka da tsarin fasahohi na dukkan filaye da dakunan yin wasanni sun dace da bukatar yin gasar wasannin Olyumpic ta Beijing, masu aikin sa kai sun taka muhimmiyar rawa sosai, an gudanar da ayyukan da abin ya shafa lami lafiya, wannan ya aza harsashi ga yin gasar wasannin Olympic ta Beijing cikin nasara.(Lami)