Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-02 15:27:00    
Wasu labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri

---- Kwanan baya yayin da rayayyen budda Shinza Tenzin Choeta na rukunin Kelzang Yeshe na addinin Budda na Tibet yake amsa tambayoyin da manema labaru suka yi masa ya bayyana cewa, hakikanan abubuwa sun tabbatar da cewa jita-jitar ra'ayin bacewar al'adun jihar Tibet da Dalai Lama na zuriya ta 14 ya baza ba ta zauna ba ko kusa. Sai a duba halin yin amfani da harshen kabilar Tibet da littattafan koyarwa da aka buga kawai, za a iya gane cewa ra'ayinsa ya cika wauta.

Mr. Shinza tenxzin Choeta wanda shi ne mataimakin direktan zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar jihar Tibet mai cin gashin kanta ya bayyana cewa, cikin shekaru da yawa da suka wuce, sassan ba da ilmi na jihar Tibet kullum suna mai da harshen kabilar Tibet a matsayin muhimmin darasi da ake yi a matakin ba da ilmi na farko. Domin cin gadon kyawawan al'adun kabilar Tibet, jihar Tibet ta yi ceto da kyautata da kuma buga manyan littattafai fiye da 260 da aka rubuta da harshen kabilar Tibet. Aikin ba da ilmi na zamani na jihar Tibet ya yalwatu daga rishinsa zuwa haifuwarsa, yaran manoma da makiyaya na jihar dukkansu suna more manufar da gwamnatin kasar ta tsayar wajen samun damar shiga makaranta a kyauta wajen abinci da gidajen kwana da kuma karatu.

---- Cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, a lardin Qinghai inda 'yan kabilu da yawa suke zama dake arewa masu yammacin kasar Sin, an dauki matakai da yawa domin ba da kariya ga fasahar jama'a ta kabilar Tibet, ta yadda aka ci gado da kuma yada fasahar kabilar Tibet sosai.

Bisa abubuwan da hukumar al'adu ta lardin Qinghai ta bayar an ce, a shekarar 2006, wato a karo na farko ne aka shigar da abubuwa 8 na al'adun kabilar Tibet na wannan lardi cikin sunayen abubuwan al'adun tarihi da aka gada daga kakanni zuwa kakanni kuma bisa matsayin kasa. Daga cikin wadannan abubuwan al'adun tarihi har da kide-kide da raye-raye, da adabi da al'adu na jama'a, da likitanci da magunguna na kabilar Tibet da kuma wasannin kwaikwayo.

Yanzu a lardin Qinghai da akwai 'yan fasaha guda 9 wadanda aka nada su da su zama magadan ayyukan abubuwan al'adun tarihi da aka gada daga kakanni zuwa kakanni bisa matsayin kasa, wadanda kuma gwamnatin kasar ta ba su kudin taimako don cin gado da kuma bunkasa irin wadannan ayyukan fasaha na gargajiya.

Cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, lardin Qinghai kuma ya rubunya kokari domin haras da manoma da makiyaya daga fannin al'adu da fasaha, ciki har da fasahar gargajiya ta yin zanen Tangka da yin kwado da linzami da wasannin wake-wake da raye-raye na kabilar Tibet.(Umaru)