Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-02 15:25:29    
A duba jihar Tibet daga tarihi

cri

Yanzu a jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin, jama'a suna mure ikon masu mulkin kasa, yawancin iyalansu suna da gidajen kwana na kullum, sabo da haka dukkan manoma da makiyaya sun shiga tsarin likitanci bisa harsashin gama karfi da samun damar ganin likita a fayu a shiyyoyin noma da kiwon dabbobi, yawan mutanen da suka samu ilmi tilas na makarantu masu tsarin karatu na shekaru 9 ya kai fiye da kashi 90 bisa 100. Amma yau da shekaru fiye da 50 da suka gabata, an tafiyar da tsarin mulkin gargajiya na manoma bayi ta hanyar haduwar siyasa da addini a nan, mutane 'yan kabilar Tibet wadanda yawansu ya kai fiye da kashi 95 bisa 100 manoma bayi ne wadanda ke zama cikin talauci kwarai.

Yanzu a cikin dakin adana kayayyakin tarihi na jihar Tibet, ana nuna wata wasikar da wani dan gata ya rubuta wa wani daban a zamanin da a jihar, a cikin wasikar ya rubuta haka, "Shekaran jiya na yi wasan karta da kai, na yi hasarar manoma bayi 3 da dawaki 7 da tsabar kudi guda 20 da aka yi da azurfa, zan kai maka da su a yau."

A zamanin da an yi canjin manoma bayi bisa matsayin kudi a jihar Tibet. Mr. Gelek, mataimakin shugaban cibiyar binciken ilmin Tibet ta kasar Sin wanda ya taba shan jurewar tarihi kamar haka ya tuna da cewa,

"Tun tuni kakata manomiyar baiwa wadda ba ta gidan wannan sarki ba ce, ta wani gidan sarki daban ce, wato ta zama abar da aka ba wa wannan sarki kyauta, sabo da haka ni ma na zo wannan gidan sarki tare da ita. Monoma bayi da yawa sun taba zama abubuwan kyauta kamar mu. An haife ni cikin garken Shanu, mamata ta haife ni da safe, amma ta je aikin kwatago da yamma, tun da ya ke mu manoma bayi ne, shi ya sa ba mu da damar samun shakatawa, ko mace mai jego ma haka ne."

A tsohon zamani a jihar Tibet, yawancin yara wadanda aka haife su ne bisa matsayin kananan bayi manoma ko bayi kawai, suna girma cikin mummunan halin jin yunwa da sanyi da tsoro, yara da yawa sun mutu sabo da yunwa da cututtuka da hadarurrukan da suka faru ba zato ba tsammani.

A wancan lokaci a jihar Tibet, yawan manoma bayi ya kai fiye da kashi 95 cikin 100 bisa jimlar mutanen jihar, wadanda suke karkashin mallakar tsirarun sarakuna iri 3 wato ma'aikatan hukuma, da masu hannu da shuni, da manyan sufaye wadanda yawansu bai kai kashi 5 cikin 100 bisa na jimlar mutanen jihar ba, amma suna mallakar dukkan gonaki da makiyayai da dazuzzuka da duwatsu da kuma yawancin dabbobin gida.

Mr. Zhou Yuan, masanin ilmin Tibet na cibiyar binciken ilmin Tibet ta kasar Sin ya bayyana cewa,

"Ainihin halin tsarin mulkin gargajiya na manoma bayi na haduwar siyasa da addini hadadden mulki ne da manyan sufaye da masu hannu da shuni suka yi wa tarin manoma bayi, sun yi kane- kane da kayayyakin kawo albarka na jihar Tibet sosai, kuma suna mallakar manoma bayi da yi musu zalunci da danniya sosai, da haka ne aka aza harsashin tsarin kawo albarka na mulkin gargajiya na manoma bayi".

Bayan shekarar 1959, bisa burin tarin jama'a talakawa da manyan mutane masu kishin kasa na jihar Tibet, an sa aya ga tsarin mulkin gargajiya na manoma bayi wanda aka gudanar da shi cikin shekaru fiye da dari a jihar Tibet, an yi aikin jaddada dimokuradiyya a jihar, da kafa gwamnatin cin gashin kanta ta kabirlar Tibet a can, daga nan ne miliyoyin manoma bayi suka zama masalautan kasa wadanda ke juya akalarsu da kansu. Mr. Gelek, mataimakin shugaban cibiyar binciken ilmin Tibet ta kasar Sin ya bayyana cewa,

"Mun tsai da cewa, aikin jaddada dimokuradiyya da aka yi a shekarar 1959 a jihar Tibet ya zama masomi ne ga ayyukan zamanintar da jihar. Me ya sa a ce haka? Dalilin kuwa shi ne, sabo da aikin nan yana da muhimmiyar ma'ana daga fannoni 3, ma'ana ta farko tana kan siyasa, wato karo na farko ne mutane marasa 'yanci sabo da tsarin danniya suka tashi tsaye suka samu ikon magana da na yin zabe. Ta 2, yawancin manoma bayi sun gane cewa zaman al'umma na da ba shi da adalci. Ma'ana ta 3 ta fi muhimmanci wato tana nufin jaddadawar tsarin gonaki, aikin jaddada dimokuradiyya da aka yi ya tattara dukkan gonaki a karo na farko kuma ya rarraba su ga dukkan mutane matalauta da manoma bayi, ta yadda suka samu gonaki na kansu."(Umaru)