Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-02 11:21:51    
Mr. Li Changchun ya kai ziyara ga lardin Sichuan domin gayar da yara

cri

Ran 1 ga watan Yuni ranar yara ta duniya, Mr. Li Changchun memban zaunanen kwamiti na ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin ya kai ziyara ta musamman ga wuraren da ke fama da bala'in girgizar kasa na lardin Sichuan domin gayar da yara da ke wuraren, da kuma ruwaita gaisuwa daga Mr. Hu Jintao babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin.

A cikin asibitin jama'a na uku na birnin Mianyang, Mr. Li Changchun ya gayar da yaran da ke karbar jiyya, ya ba da musu kwarin gwiwa da su kara yin limani domin raya jiki da sauri.

Ban da haka kuma, Mr. Li Changchun ya ba da akwatin rediyo dubu 100 da wasu kayayyakin karatu na yara da hukumomin kwamitin tsakiya suka gabata, ya ba da kwarin gwiwa ga yara da su kara yin kokarin karatu domin sami ilmi masu yawa, da kuma sake gina gidaje tare.