Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-02 10:58:51    
Wani jirgin sama mai saukar ungulu na dakarun yaki da bala'in girgizar kasa da ceton mutane na kasar Sin ya fado kasa

cri
Wani jirgin sama mai saukar ungulu mai aikin jigilar kayayyaki na rundunar sojan yaki da bala'in girgizar kasa da ceton mutane ta yankin soja na Chengdu na kasar Sin ya fado kasa yayin da yake kokarin gudanar da aikin ceton mutanen da bala'in girgizar kasa ya ritsa da su a shekaranjiya wato ranar 31 ga watan Mayu. Bayan da shugaban kasar Sin, kuma shugaban kwamitin soja na tsakiyar kasar Sin Hu Jintao ya samu wannan labari, ya bada umurnin ceton mutanen da abin ya shafa ba tare da bata lokaci ba.

Da kusan karfe 3 na yamma, sakamakon sauyawar yanayi ta ba-zata, wannan jirgin sama mai aikin jigilar masana ilimin riga-kafin yaduwar cututtuka zuwa gundumar Li ta lardin Sichuan ya fado kasa yayin da yake dawowa gida a wani wurin dake kusa da garin Yingxiu na gundumar Wenchuan.

Bayan da shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya samu labarin, ba tare da wani jinkiri ba, ya aika da mataimakin shugaban kwamitin soja na tsakiyar kasar Sin Guo Boxiong zuwa wurin domin jagorantar aikin ceton mutane.

A halin yanzu an riga an tabbatar da cewar, gaba daya dai akwai mutane 19 wadanda ke cikin wannan jirgin sama mai saukar ungulu, ciki har da masu tukin jirgin guda 5, da mutanen da suka ji rauni wadanda ake jigilarsu da dai sauran mutane guda 14. Zuwa karfe 7 na daren jiya wato ranar 1 ga wata, ba'a gano wannan jirgin sama da mutanensa ba.(Murtala)