|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2008-06-01 19:39:54
|
Mutane 69016 sun rasa rayukansu a sakamakon babbar girgizar kasa da ta auku a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan
cri
Ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayar da sanarwa a yau 1 ga wata da yamma cewa, ya zuwa ranar 1 ga wata da karfe 12, mutane 69016 sun rasa rayukansu a sakamakon babbar girgizar kasa da aka samu a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan.
Ya zuwa ranar 1 ga wata da karfe 12, mutane 368545 sun ji rauni a sanadiyar bala'in girgizar kasar, yayin da 18830 suka bace.
Ya zuwa ranar 1 ga wata da karfe 12, kasar Sin ta samu taimakon kudi da na kayayyakin da ke da darajar kudin Sin RMB biliyan 41. 5 daga bangarori daban daban na gida da na waje, kuma an riga an bayar da taimakon kudi da na kayayyaki da ke da darajar kudin Sin RMB sama da biliyan 11.5. ga yankuna masu fama da bala'in. (Bilkisu)
|
|
|