Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-31 22:05:51    
(Sabunta)Hu Jintao ya yi rangadin aiki a Shaanxi

cri

Ran 31 ga watan Mayu, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya je gundumar Ningqiang da ke fama da girgizar kasa a lardin Shaanxi, inda ya gana da jama'ar da ke fama da bala'in girgizar kasa. Ya taya wa yaran da ke zama a wuraren da ke fama da girgizar kasa da yara manyan gobe na duk kasar Sin da kuma ma'aikatan koyar da yara murnar ranar yara ta duniya ta ran 1 ga watan Yuni.

Ya kasance da tsawon kilomita fiye da 200 daga gundumar Ningqiang zuwa ta Wenchuan ta lardin Sichuan, gundumar Ningqiang ta samu bala'in girgizar kasa sosai, a ran 27 ga watan Mayu kuma, an sake samun girgirzar kasa da karfinta ya kai awo5 da digo 7, wannan ya kara wahalar jama'a.

Mr. Hu ya ce, tabbas ne Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da kuma gwamnatin kasar Sin za su tsugunar da jama'a da kyau bisa hanyoyi daban daban, haka kuma tabbas ne za su taimakawa jama'ar da ke fama da bala'in girgizar kasa wajen maido da ayyukansu, da sake gina gidajensu. Mr. Hu ya yi imani cewa, bisa goyon baya daga Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da kuma gwamnatin kasar Sin, da taimakon kasar dukkan jama'ar kasar Sin suke bayarwa, da kuma kokarin da jama'ar suke yi da kansu, za a iya daidaita matsalolin da suke fuskanta a halin yanzu, za su iya samun kyakkyawan zaman rayuwa a nan gaba.(Danladi)