Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-31 20:51:22    
Mutane 68977 sun mutu sakamakon girgizar kasa da ta auku a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan

cri

Ran 31 ga watan Mayu, bisa labarin da ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayar, bisa umurnin babban ofishin ba da umurni kan fama da girgizar kasa da gudanar da ayyukan ceto na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, an ce, ya zuwa karfe 12 na ran 31 ga watan Mayu da rana, bala'in girgizar kasa da ta auku a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin ya riga ya yi sanadiyar mutuwar mutane 68977 yayin da mutane fiye da dubu 367 suka jikata, kuma mutane 17974 suka bace, an tsugunar da mutane fiye da miliyan 15.14, yawan mutanen da ke fama da bala'in ya kai fiye da miliyan 45.54.

Ya zuwa karfe 12 na ran 30 ga watan Mayu da dare, an riga an ceci mutane da kuma kaurar da su fiye da dubu 780, da kuma kubutad da mutane 6541 daga kangaye.

Ban da wannan kuma ya zuwa karfe 12 na ran 31 ga watan Mayu da rana, yawan mutanen da suka samu jiyya a cikin asibitoci domin jin rauni a cikin girgizar kasa ya kai kusan dubu 90, kuma a ciki an sallame su dubu 60 daga asibitocin, haka kuma birnin Chongqing da dai sauran larduna 20 sun karbi 'yan lardin Sichuan masu jikata 9245.

Bugu da kari kuma ya zuwa karfe 12 na ran 31 ga wata da rana, kasar Sin ta kebe kudaden Sin Yuan biliyan 22.5 wajen fama da bala'in girgizar kasa. Yawan kudade da kayayyakin taimako da kasar Sin ta samu daga gida da waje ya kai fiye da Yuan biliyan 40.1.(Danladi)