Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-31 19:45:47    
An kammala aikin mika wutar yola na rana ta farko a lardin Hubei

cri

A ranar 31 ga watan Mayu, cikin nasara ne, aka kammala aikin mika wutar yola ta gasar wasannin Olympics ta Beijing na rana ta farko a lardin Hubei da ke tsakiyar kasar Sin.

A wannan rana, an mika wutar yola ne a birnin Wuhan, babban birnin lardin Hubei, zakaran wasan lankwashe jiki na gasar wasannin Olympics Mr. Yang Wei ya zama mai rike da wutar yola na farko a wannan karo. An fara mika wutar yola da karfe 8 na safe, duk tsawon hanyar ya kai kilomita 19.9.

Kafin a fara mika wutar yola, dukkan jama'ar da suka shiga cikin aikin mikawa wutar yola sun shirya bikin jimani, domin nuna ta'aziyya ga wadanda suka mutu sakamkon girgizar kasa a gundumar Wenchuan.

Daga ranar 1 zuwa 2 ga watan Yuni, za a mika wutar yola a biranen Yichang, da Jingzhou na lardin Hubei.(Danladi)