Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-31 16:59:00    
Jia Qinglin ya yi rangadin aiki a wuraren da ke fi fama da girgizar kasa

cri
Ran 30 ga wata, Jia Qinglin, zaunannen mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ya je garin Yingxiu da birnin Dujiangyan da sauran wuraren da ke fi fama da mummunar girgizar kasa ta Wenchuan daya bayan daya, inda ya dudduba halin da wadannan wurare ke ciki da kuma ba da jagoranci ga ayyukan fama da girgizar kasa.

Ran 30 ga wata da safe, Mr. Jia ya je garin Yingxiu, inda cikin halin aminci ne ya gana da fararen hula da ke fama da girgizar kasa da kuma 'yan sanda da hafsoshi da sojojin da ke gudanar da ayyukansu, ya kuma yi wa fararen hula da ke fama da girgizar kasa bayani da cewa, yana fatan za su yi gwagwarmaya domin kubutad da kansu, ta haka za su samar da kyakkyawar zaman rayuwa a nan gaba. Daga baya kuma Mr. Jia ya je wuraren tsugunar da wadanda suke fama da girgizar kasa a birnin Dujiangyan domin ganawa da 'yan makaranta cikin halin aminci. Ya gaya wa yara cewa, dukkansu na da zuciya mai karfi. Yanzu ranar yara ta duniya tana kan hanya, shi ya sa ya taya wa 'yan makarantar murnar ranar yara ta duniya. A ran nan da yamma, Mr. Jia ya je cibiyar ba da agaji da ke birnin Guanghan domin ganawa da ma'aikata da masu aikin sa kai cikin halin aminci.(Tasallah)