Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-31 16:34:50    
Gwamnatin kasar Sin ta yi nazari kan yadda za a iya yin amfani da kayayyaki da kudade na jin kai bisa doka

cri
A ran 30 ga wata, Mr. Wen Jiabao, firayin minista, kuma babban kwamandan hedkwatar ba da umurni ga aikin fama da bala'in girgizar kasa da ceto mutane ta majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shugabanci wani taro a birnin Beijing, inda aka yi nazari kan yadda za a yi amfani da kayayyaki da kudade na jin kai bisa doka kamar yadda ya kamata.

A gun taron, an nemi a bi ka'idar "wani ya ba da kayayyaki ko kudade na jin kai da kansa, a yi amfani da kayayyaki da kudade na jin kai domin aikin fama da laba'in musamman, kuma dole ne a tsara shirin rarraba su tare, har ma dole ne a sa ido kan yadda ake amfani da su" lokacin da ake tafiyar da aikin yin amfani da kayayyaki da kudade na jin kai domin tabbatar da za a iya yin amfani da dukkan kayayyaki da kudade na jin kai kan ayyukan fama da bala'in girgizar kasa da ayyukan sake raya yankuna masu fama da bala'in.

A waje daya kuma, Mr. Hui Liangyu, mataimakin firayin minista, kuma mataimakin babban kwamandan hedkwatar ba da umurni ga aikin fama da bala'in girgizar kasa da ceto mutane ta majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shugabanci wani taro a lardin Sichuan, inda ya saurari ra'ayoyin da masana suka bayar kan yadda za a sake raya yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa da ya auku a Wenchuan na lardin Sichuan. Mr. Hui ya jaddada cewa, dole ne gwamnatocin yankunan da ke fama da bala'in da hukumomin da abin ya shafa su nemi ra'ayoyi daga masana, kuma su bi ra'ayoyin kimiyya, har ma su dogara da fasahohin zamani lokacin da suke fama da bala'in girgizar kasa. (Sanusi Chen)