Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-30 18:55:18    
Sabunta: Mr. Yang Jiechi ya yi gaisuwa ga kungiyoyin jiyya na kasashen waje wadanda ke taimakawa wuraren bala'i

cri

Ran 30 ga wata, Mr. Yang Jiechi ministan harkokin waje na kasar Sin wanda ke yin ziyara a wuraren da ke fama da bala'in girgizar kasa tare da Mr. Lee Myung Bak shugaban kasar Korea ta kudu ya yi gaisuwa ga kungiyoyin jiyya na kasashen Birtaniya, da Cuba, da Japan, da Rasha, da Jamus wandanda ke ba da taimako a wuraren da ke fama da bala'i.

A wannan rana kuma, Mr. Yang Jiechi ya yi godiya da gaisuwa ga kungiyoyin jiyya na kasashen Faransa da Italiya ta hanyar waya.

Mr. Yang Jiechi ya nuna cewa, yayin da aka samu matsanancin bala'in girgizar kasa a lardin Sichuan na kasar Sin, kasashen duniya sun nuna goyon baya da taimako masu daraja, kuma wasu kasashe sun aiko da kungiyoyin jiyya da sauri, kuma sun ba da agaji ga dubban mutanen da suka jikkata. Wannan ya nuna amincewar da ke tsakanin jama'ar kasashen Sin da kasashe dabam daban da ainihin jin kai, kuma sun ba da gudummowa sosai ga ayyukan tinkarar bala'i. kuma sun sami yabo sosai daga mutanen da ke wurin da takwaransu na kasar Sin saboda ainihin sadaukarwa da fasahohinsu. Mr. Yang Jiechi ya wakilci gwamnati da jama'ar kasar Sin domin yi musu godiya da gaisuwa.