Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-30 17:03:54    
Shirin musamman na murnar cika shekaru 45 da sashen Hausa na rediyon kasar Sin

cri

Jama'a masu sauraro, assalamu alaikum, barkanku da war haka, barkanmu kuma da sake saduwa da ku a filinmu na amsoshin wasikunku, inda yau za mu ci gaba da gabatar muku shirinmu na "waiwaye adon tafiya", wato shirin musamman na murnar cika shekaru 45 da sashen Hausa na rediyon kasar Sin ya fara aiki, kuma ni ce Lubabatu ke gabatar muku da wannan shiri daga nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin.

Masu sauraro, yau na gayyaci takwaran aikina kuma shugaban sashen Hausa, Sanusi zuwa filinmu na "waiwaye adon tafiya", don mu tattauna da shi tarihinsa na aiki da sashen Hausa da kuma makomar sashen Hausa.

Lubabatu:To, malam Sanusi, maraba da zuwa filinmu na "waiwaye adon tafiya".

Sanusi: Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, ni ne Sanusi Chen.

Lubabatu: Na san ka dade kana aiki a nan sashen Hausa, shi ya sa ina tsammani ta muryarka ne masu sauraronmu za su iya gane kai wane ne, amma duk da haka, ko za ka iya gabatar da kanka zuwa ga masu sauraronmu? Daga ina ne ka fito kuma yaushe ne ka fara aiki a sashen Hausa?

Sanusi: An haife ni a shekarar 1966 a lardin Jiangsu da ke gabashin kasar Sin, kuma a shekarar 1990, na fara aiki a sashen Hausa na rediyon kasar Sin.

Lubabatu:Duk lokacin da Hausawa suka ji Sinawa na iya Hausa, su kan ji mamaki sosai, shi ya sa watakila yanzu masu sauraronmu na sha'awar a ina ne ka koyi Hausa, ko a wata kasar Afirka?

Sanusi: A shekarar 1985, na ci jarrabawar shiga jami'ar koyon harsunan waje ta Beijing, domin koyon harshen Hausa. Bayan da na gama karatu daga wannan jami'a, tun daga watan Mayu na shekarar 1994 har zuwa watan Mayu na shekarar 1995, na kara koyon harshen Hausa a jami'ar Ahmed Bello, da ke Samaru, Zaria.

Lubabatu:To, wato bayan da ka gama karatu a jami'ar koyon harsunan waje ta Beijing, sai ka fara aiki a sashen Hausa na rediyon kasar Sin.

Sanusi: Haka ne.

Lubabatu:To, me ya sa bayan da ka gama karatu a jami'a, sai ka zabi sashen Hausa na rediyon kasar Sin ka yi aiki da shi?

Sanusi: Sabo da sashen Hausa na rediyon kasar Sin yana aiki domin sada zumunta a tsakanin jama'ar kasar Sin da 'yan Afirka, kuma kasashen Afirka suna da al'adu iri daban daban, ina sha'awarsu sosai, sabo da haka, na zabi sashen Hausa na CRI, na fara aiki da shi.

Lubabatu:To, na san ka taba zuwa Nijeriya har sau da dama, wani lokaci domin aiki, wani lokaci domin karatu, ko za ka iya dan bayyana mana ziyararka a Nijeriya?

Sanusi: Ya zuwa yanzu na riga na kai ziyara a kasar Nijeriya har sau uku, tun daga watan Mayu na shekarar 1994 har zuwa watan Mayu na shekarar 1995, na je Nijeriya domin kara koyon harshen Hausa.

Lubabatu:A jami'ar ABU?

Sanusi: E, a jami'ar ABU. Sa'an nan, tun daga shekarar 2002 har zuwa 2004, na yi aiki a ofishin CRI da ke birnin Ikko, domin watsa labaran Afirka. Sa'an nan kuma, a shekarar 2005, na sake zuwa Nijeriya, domin ganawa da masu sauraronmu a Kano.

Lubabatu:To, dazun nan ka ce, daga shekarar 2002 har zuwa 2004, ka taba aiki a Nijeriya, wato a ofishinmu a birnin Ikko. Na san a lokacin, diyarka karama ce, ko?

Sanusi: E, tana da shekara daya da watanni takwas kawai da haihuwa.

Lubabatu:Kai, gaskiya karama ce.

Sanusi: Karama sosai.

Lubabatu:Ko kana begenta, sabo da tsawon lokaci ne, kuma akwai nisa sosai.

Sanusi: Tabbas ne ina begenta sosai, sabo da haka, na je Nijeriya tare da hotunanta, kuma kusan kowane mako, na buga mata waya, a cikin waya, na ji muryarta.

Lubabatu:Ko ta san inda babanta ya tafi?

Sanusi: Da farko dai, ba ta sani ba, sabo da karama, amma bayan wasu watanni, ta fara sani, ta kan gaya wa abokanmu, babanta ya je Afirka.

Lubabatu:Bayan da ka dawo daga Nijeriya, shekarunta nawa ne?

Sanusi: Kusan hudu.

Lubabatu:Ko a lokacin, ta san ka?

Sanusi: Ba ta sani sosai ba, amma ta san babanta ya dawo.

Lubabatu:Yau shekaru kusan 20 ke nan kana aiki a sashen Hausa, ko akwai abubuwan da suka burge ka har ba za ka iya mantawa da su ba?

Sanusi: Abubuwan da suka burge ni suna da yawa, kamar lokacin da nake aiki a kasar Nijeriya kuma nake karatu a Nijeriya, daliban ABU sun taimake ni sosai wajen koyon harshen Hausa, kuma lokacin da nake aiki a can, masu sauraronmu su kan taimake ni wajen ganawa da masu sauraronmu a Kaduna da kuma a Kano kuma a Abuja, kuma kullum suna buga mini waya, inda suka ba ni shawarar kyautata shirinmu.

Lubabatu:To, sashen Hausa na tuntubar masu sauraronsa a kullum, kuma mu kan je Nijeriya ko Nijer don ganawa da masu sauraronmu a kai a kai, na san kuma kamar yadda ka fada dazun nan, a shekarar 2005, ka taba ganawa da masu sauraronmu a Nijeriya, ko za ka yi mana bayani a kan ganawar?

Sanusi: Hakika dai, na taba ganawa da masu sauraronmu har sau biyu, karo na farko shi ne a shekarar 2003, a watan Afril, na gana da masu sauraronmu a Kaduna kuma a Kano, a lokacin can, malam Baban Dada ya taimake ni sosai, ya kira wasu masu sauraronmu, mun yi taro tare a cikin ofishinsa, sa'an nan kuma, na je Kano, masu sauraronmu sun je sun gana da ni, mun yi musanyar ra'ayoyi a kan shirye-shiryen sashen Hausa na CRI, kuma sun nuna mana godiya sosai, domin suna samun labaran kasar Sin ta rediyonmu.

Lubabatu: Ba a iya raba bunkasuwar sashen Hausa da goyon bayan da masu sauraronsa suke bayarwa, a matsayina na mai gabatar da shirin "amsoshin wasikunku", kullum na kan sami dimbin wasiku daga hannun masu sauraronmu, wadanda suka mika mana gaishe-gaishensu da shawarwarinsu, gaskiya sun burge ni sosai da sosai, kuma duk lokacin da na karanta wasikunsu, na kan sami kwarin gwiwa sosai?

bisa goyon bayan masu sauraronmu, a cikin shekaru 45 da suka wuce, sashen Hausa ya bunkasa sosai, da ma lokacin da aka kafa sashen Hausa, tsawon shirye-shiryen da yake gabatarwa a kowace rana ya kai rabin awa ne kawai, amma yanzu lokacin ya tsawaita kwarai da gaske.

Sanusi: Haka ne, yanzu kowace rana, muna watsa shirye-shirye na tsawon awa hudu, musamman bayan mun kafa rediyon FM a Afirka.

Lubabatu: kamar yadda ka fada, tun daga shekarar 2006, mun fara bude rediyon FM a birnin Yamai na kasar Nijer, kuma daga baya, a wannan filinmu na "amsoshin wasikunku", na kan sami wasikun masu sauraronmu da ke mana tambaya, wato yaushe ne za mu bude rediyon FM a kasarsu ta Nijeriya? To, yanzu a wannan hirar da muke yi, ko za ka amsa musu tambayar?

Sanusi: Yanzu muna tsara irin shiri na kafa FM a kasar Nijeriya, amma dole ne mu bi dokar Nijeriya, idan gwamnatin Nijeriya ta yarda da mu kafa rediyon FM a kasarsu, ba shakka, za mu kafa irin wannan rediyon FM. Amma idan ba za mu iya samun izni ba, shi ke nan.

Lubabatu:To, sai idan Allah ya yarda.

Sanusi: Yauwa.

Lubabatu:Na san a shekarar 2003 ne sashen Hausa ya soma kaddamar da shafinsa na internet, wato hausa.cri.cn, to, shin a lokacin, me ya sa ya kaddamar da shafin?

Sanusi: Sabo da a cikin shekaru 45 da suka gabata, sashen Hausa ya sami cigaba cikin sauri, kuma a cikin shekaru 10 da suka wuce, gidan rediyon kasar Sin ya sami cigaba wajen yanar gizo. Tun daga shekarar 1998, ya soma watsa labarai da shirye-shiryensa a kan shafuffukansa na internet, da harshen Sinanci da Turanci da Larabci da Jamusanci da harshen Spain da Rashanci da Faransanci da na Koriya da harshen Portugal da dai sauran harsunan waje. A waje daya kuma, kasashen Afirka sun sami cigaban shafuffukan yanar gizo, sabo da haka, a watan Oktoba na shekarar 2003, sashen Hausa ya bude shafin yanar gizo, inda ya watsa labaran kasar Sin da na sauran kasashen duniya, da sauran shirye-shiryenmu, kamar su kananan kabilun kasar Sin da wasanin motsa jiki da tattalin arzikin kasar Sin da yawon shakatawa a kasar Sin da al'adun kasar Sin da Beijing a shekarar 2008 da amsoshin wasikunku da Sin da Afirka, Bisa kididdigar da aka yi, yanzu yawan karatun shafinmu na internet ya kai kimanin dubu 80 a kowane wata.

Lubabatu:Har dubu 80, gaskiya ya sami karbuwa. Muna kuma fatan masu sauraronmu za ku dinga ziyartar shafinmu na internet, ku ba mu shawarwarin kyautata shi, kada kuma ku manta, adireshinmu shi ne hausa.cri.cn.

A ran 1 ga watan Yuni na wannan shekara, sashen Hausa na rediyon kasar Sin zai cika shekaru 45 da kafuwa, shin a kusantowar wannan muhimmiyar rana mai farin ciki, kana da abin da kake son fada?

Sanusi: A lokacin da muke taya murnar cika shekaru 45 da kafa sashen Hausa na rediyon kasar Sin, tare da dimbin gaisuwa da fatan alheri a gare ku, muna fatan kuna nan lafiya kamar yadda muke a nan Beijing, kasar Sin. Haka kuma muna fatan masu sauraronmu za ku ci gaba da sauraronmu kamar yadda kuke yi, kuma za ku iya cigaba da aiko mana takardunku, don isar mana ra'ayoyinku game da shirye-shiryenmu. Ina cike da imanin cewa, bisa goyon bayanku, sashen Hausa na rediyon kasar Sin zai kara samun cigaba, idan Allah ya yarda.

To, masu sauraro, wannan shi ya kawo karshen shirinmu na yau, amma kada ku manta, a makon gobe war haka, za mu ci gaba da kawo muku shirye-shiryenmu na "waiwaye adon tafiya", da haka ni Lubabatu daga nan Beijing ke cewa, "sai Allah ya kai mu ranar Jumma'a mai zuwa. (Lubabatu)