Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-29 20:40:02    
Mutane masu ceto da kayayyakin agaji da tsakiyar Asiya da kasashen Korea ta Kudu da kuma Belgium suka samar sun iso Sin

cri
A ran 29 ga wata da sassafe, kayayyakin agaji ton 170 da kasar Kyrgyzstan ta samar sun isa tashar jirgin kasa ta birnin Tianshui na lardin Gansu na kasar Sin.

An labarta cewa, wadannan kayayyakin agaji da nauyinsu ya kai ton 170 su ne tantuna da na'urorin dafa abinci masu yin amfani da wutar lantarki da dai sauran kayayyakin da yankuna masu fama da girgizar kasa ke bukata cikin gaggawa. A 'yan kwanaki masu zuwa, kayayyakin agaji wajen ton 1300 da kasashen Kazakhstan da Turkmenistan da kuma Tajikistan suka samar za su isa birnin Tianshui.

Ban da wannan kuma, a ran 29 ga wata da tsakar rana, kyayyakin taimako ton 26.6 da bangaren sojojin kasar Korea ta Kudu ta samar sun isa birnin Chengdu ta jirgin sama, wadanda suke hada da tantuna da tufafi da barguna da kuma abinci.

Haka kuma a ran 29 ga wata da sassafe, mutane da kayayyakin taimako na rukuni na biyu da gwamnatin kasar Belgium ta samar don tallafa wa kasar Sin wajen fama da girgizar kasa sun riga sun isa birnin Shanghai.(Kande Gao)