Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-29 17:00:53    
Wani furofesa musulmi mai zurfin ilimi na kabilar Kirgiz

cri

A da 'yan kabilar Kirgiz wadanda aka fi samunsu a jihar Xinjiang mai cin gashin kai ta kabilar Uigur da ke yammacin kasar Sin su makiyaya ne. A cikin shekarun nan, sun samu damar samun ilimi, yanzu mutane da yawa daga cikinsu ba za su yi harkokin kiwon dabobi ba, sun zama lauyoyi da 'yan kasuwa da kuma masu ilimi. A cikin shirinmu na yau, muna so mu gabatar muku da wani furofesa musulmi mai zurfin ilimi na kabilar Kirgiz wanda ake kiransa Mr. Marc Lake.

Yayin da muka ganin furofesa Marc Lake, har mun kasa gaskata abin da ke gabanmu, wannan furofesa mai farin gashi da ke yin murmushi kullum, a hakika dai shekarunsa da haihuwa bai kai 50 ba. Kuma a cikin ofishinsa, ban da wata na'urar kwamfuta da wani teburi da kuma wani taliho, sauran abubuwan da suka fi yawa su ne littattafai. Furofesa ya yi murmushi kuma ya ce, yana son zaman rayuwa mai sauki. Ya gaya mana cewa, "Game da zaman son abin duniya, a ganina, muddin kayayyakin zaman yau da kullum suna iya biyan bukatun zama mai sauki, to ya isa. Kamata ya yi dan Adam ya yi sha'anin da ke so da kuma yin abubuwa masu ma'ana domin ba wa zuriyoyi abubuwa masu amfani."

Furofesa Marc Lake ya samu sakamako mai kyau a fannin yin nazari kan harshen Kirgiz, ya shirya da kuma fassara lattattafai da yawa game da kabilar Kirgiz. Kuma furofesa yana kaunar garinsa da kabilarsa sosai. A ganinsa, harshe ba hanya ce kawai da ake yin amfani da shi domin yin mu'amala tsakaninsu ba, har ma zai taka muhimmiyar rawa ga abin da ake yi da kuma abin da ake tunani a cikin kwakwalwa. Shi ya sa yin nazari kan harshe na wata kabila, yana da muhimmiyar ma'ana kan samun fahimtar tarihin kabilar da kuma bunkasuwarta a nan gaba. Ya ce, "Yara sun san wannan duniya tun lokacin da suka fara koyon harshe. Yawancin 'yan kabilar Kirgiz suna yin zama a cikin yankunan da ke kan duwatsu, shi ya sa tun daga lokacin yarantakarsu ba su da dama da yawa domin yin mu'amala da waje. A cikin halin nan da ake ciki, ko shakka babu iyaye sun zama malamai na farko na yaransu, maganganun da iyaye suke yi suna ba da tasiri ga yaransu har a duk tsawon rayuwarsu."

A gun wani taron kara wa juna ilmi na duniya, jawabin da Mark Lake ya yi kan kabilar Kirgiz ya jawo hankulan masu halartar taron. Daga baya kuma ba kawai shugabannin kasar Kirghiziastan sun gana da shi ba, har ma wani kwalejin al'adun harsuna na kasar ya nada shi da ya zama shehun malamin da aka daukaka sunansa.

Mark Lake shi kuma kwararre ne wajen yin nazari kan wakar gargajiyar tarihi ta kabilar Kirgiz wadda ake kiranta Manas. Wakar Manas ta gaya mana labarai kan cewa mutanen iyalin Manas na zuriyoyi takwas suka yi dagiya da hare-haren da sauran kabilu suka kai musu domin kare garinsu da kuma neman zaman lafiya da zaman karko na kabilar Kirgiz, shi ya sa tana da daraja sosai a fannonin fasaha da kuma al'adun gargajiya. Furofesa Mark Lake ya taba buga makala fiye da goma game da wakar tarihi ta Manas, ban da wannan kuma ya mai da hankalinsa a kan buga wakar ta harafofi da dama.

Aikin yin narazi kan harshe yana da wuya sosai, yana bukatar sanin ilmi na fannoni daban daban. Yawan 'yan kabilar Kirgiz da ke jihar Xinjiang bai kai dubu 150 ba, kuma yawancinsu suna yin zamansu ne cikin yankuna da ke kan iyakar kasar Sin. Wani lokaci kuma, domin fahimtar wata kalma ko wani labari, Mark Lake ya kan ketare duwatsu don neman mutanen da abin ya shafa. Ko da yake Mark Lake ya sha wahaloli da yawa don wannan, amma bai ce kome ba, yana jin farin ciki sosai.

Yanzu furofesa Mark Lake shi ne babban sakatare na kungiyar nazarin al'adun gargajiya da tarihi na kabilar Kirgiz ta jihar Xinjiang, shugaban kamfanin buga mujalla da ake kira Harshe da Fassarawa na jihar Xinjiang kuma babban sakatare na kungiyar yin nazarin Manas ta kasar Sin. Sabo da haka kullum yana shan aiki sosai. A idon abokan aiki da iyalinsa, ya zama mai aiki tukuru, wato wanda bai san gajiyar aiki ba. Matarsa ta gaya mana wani labari game da shi. "A wata rana da yamma, wani abokin aikinsa ya gaya mini cewa, Mark ba shi da lafiya, rai a hannun Allah. Da jin haka, na ji tsoro sosai, nan da nan na gudu zuwa ofishinsa. Bayan da ya ga likita, likita ya ce, kwakwalwarsa ta gaji sosai, shi ya sa yake bukatar hutawa. Kuma yayin da yake cikin asibiti, kullum yana tabo batun buga littattafai."

A cikin gidan furofesa Mark Lake, ba a ajiye kayayyakin daki da yawa ba. Kuma ana iya ganin littattafai masu yawa kwarai a cikin wannan dakin da murabba'insa bai kai mita 60. Dansa ya gaya mana cewa, babansa ya yi amfani da kusan dukkan kudinsa don sayen littattafai da kuma yin nazari. Kuma ya ce, "Babana ya riga ya rubuta littattafai da yawa. Ban da wannan kuma yana so ya ba da taimako ga saura."

Yayin da muke yin hira tare da iyalin furofesa, furofesa ya riga ya yi barci. 'yarsa ta gaya mana cewa, jiya babanta ya yi ta yin aiki har duk dare. Kuma ya yi amfani da yawancin lokacinsa kan tarawa da yin bincike kan littattafai. Kuma ta ce, abubuwan da babansu ya yi sun ba da tasiri gare ta da 'yan uwanta a fannoni da yawa. Bayan da ta gama karatunta daga jami'a, tana so ta koma garinta don yin aikin koyarwa domin ba da taimako ga yaran wurin da su fitar da wannan yankin kan duwatsu daga jahilci. Ta gayawa wakilinmu cewa, "Maganar da ya fada wadda ta fi daukan hankalina ita ce tabbas ne mutum ya kansance mai ilmi. Tun daga lokacin yarantakata har zuwa yanzu, na rike ta sosai."