Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-29 17:00:59    
Masu sauraro goma sun buga waya, ko aiko mana e-mail, inda suka nuna gaisuwa ga jama'ar yankuna masu fama da bala'in

cri

A shekarar da ta wuce, masu sauraron rediyonmu daga kasashen ketare da yawansu ya kai goma, sun samu lambar yabo ta musamman a cikin gasar kacici-kacici ta jarrabawar ilmin yawon shakatawa a lardin Sichuan da muka shirya, wato 'Garin Panda, lardin Sichuan', kuma sun kai ziyara a lardin Sichuan na kasar Sin, bisa gayyatar da muka yi musu. Wuware masu kyau, da kaunar da jama'ar lardin suka nuna musu, sun burge wadannan masu sauraromu sosai. Bayan da aka samu babbar girgizar kasa a ranar 12 ga wata a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan, daya bayan daya, wadannan masu sauraro goma sun buga waya, ko aiko mana e-mail, inda suka nuna gaisuwa ga jama'ar yankuna masu fama da bala'in. Sun bayyana cewa, sun yi imani da cewa, ko shakka babu jama'ar kasar Sin za su samu nasara wajen yaki da bala'in girgizar kasa, kuma a nan gaba ba da dadewa ba, za su sake raya wani lardin Sichuan da zai fi kyau bisa na da. Yanzu, ga cikakken bayani:

Bayan da Malam N. Bala Kumar, wato mai sauraronmu daga kasar India ya samu labari game da aukuwar babbar girgizar kasa ta lardin Sichuan, nan da nan ya buga waya ga rediyonmu, don fahimtar halin bala'in da ake ciki. Ya ce, "Na yi mamaki sosai bayan da na samu labarin, sunan "Sichuan" suna ne da na saba ji. A lokacin da nake yawon shakatawa a lardin Sichuan a shekarar da ta wuce bayan da na samu lambar yabo ta musamman a cikin gasar kacici-kacici, muhalli mai zaman alhari a can ya burge ni sosai. Amma, yanzu jama'ar yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa suna shan wahala, ina jin bakin ciki sosai kan wannan."

Ya zuwa ran 26 ga wata da safe da karfe 12, girgizar kasa da ta auku a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan ya riga ya yi sanadiyar mutuwar mutane 65080, yayin da mutane dubu 360 suka jikata, kuma mutane 23150 suka bace. Mai sauraronmu daga kasar Romania Dumitru Marin ya ce, yana fatan nuna juyayi ta rediyon kasar Sin ga wadanda suka rasa rayukansu a sakamakon bala'in.

"Bayan awa daya kawai da aka samu girgizar kasa, sai na samu labarin daga gidan talibiji na Romania. Ni, da iyalina da abokaina, da kuma abokan aikina, mun yi gaisuwa ga mutanen yankuna masu fama da bala'in, musamman ma yara, kuma mun yi jimami sosai ga wadanda suka rasa rayukansu,"

Malam Novikov Egeny, mai sauraronmu daga kasar Rasha, da malam Dieter Gerhard Leupold daga kasar Jamus, da kuma malam Samdanmunkh Baatar daga kasar Mongolia, sun buga waya ko aiko mana e-mail, inda suka bayyana cewa, suna jin bakin ciki kan bala'in da aka samu a lardin Sichuan na kasar Sin. Suna fatan mutanen da aka rutse su a sakamakon girgizar kasar, za su iya fita daga hali mai hadari tun da wuri."

Bala'in da aka samu a lardin Sichuan, shi ma ya jawo hankalin Luca Bresciani, wato mai sauraronmu daga kasar Italiya.

A 'yan kwanakin da suka wuce, kullum yana kulawa da sabon cigaba da kasar Sin ta samu wajen yaki da bala'in ta tashar internet ta rediyon kasar Sin.

"Na riga na ga shirin musamman kan girgizar kasa ta lardin Sichuan da sashen harshen Italiya na rediyon kasar Sin ya kafa a tashar internet, sun bayar da labaru a dukkan fannoni kuma cikin lokaci, bayan haka kuma, sun bayar da rahotanin da abin ya shafa da yawa, wannan ya zama wata muhimmiyar hanya wajen fahimtar halin bala'in da Sichuan ke ciki. Ina fatan jama'ar kasar Sin, musamman ma jama'ar lardin Sichuan za su samu nasara wajen yaki da bala'in."

Bayan aukuwar girgizar kasa ta lardin Sichuan, gwamnatin kasar Sin ta gudanar da manyan ayyukan ceto cikin sauri, shugabannin kasar, Hu Jintao, da Wen Jiabao, da dai sauransu, sun je yankuna masu fama da bala'in, don jagorancin ayyukan ceto, yanzu kuma ana ta yin jigilar kayayyaki da yawa zuwa yankuna masu fama da bala'in. Mai sauraronmu daga kasar Morocco, malam Idriss Bououdina ya ce, amsar da gwamnatin kasar Sin ta bayar cikin sauri, ta burge shi sosai.

"Kullum gwamnatin kasar Sin na yin kokari tare da jama'arta a ko wane lokaci mai tsanani. Ina jin dumi a zuciyata a lokacin da na ga gaisawar da shugaba Hu Jintao na kasar Sin ke yi wa jama'ar yankuna masu fama da bala'in, da kulawa da sauran shugabannin kasar Sin ke yi wa jama'ar yankunan. Lallai, na sani, ko shakka babu jama'ar kasar Sin za su kau da bala'in, kuma a nan gaba ba da dadewa ba, za mu ga wani sabon lardin Sichuan na zamani kuma mai kyau."

Yanzu, ana ta cigaba da ayyukan yaki da bala'in girgizar kasa, ciki har da ceto, da sake tsugunar da jama'a masu fama da bala'in, da hana yaduwar ciwace-ciwace, da dai sauransu.

Ban da yin addua ga jama'ar kasar Sin da ke fama da bala'in kuma, wasu daga cikin wandannan masu sauraronmu goma daga cikinsu da suka taba yin yawon shakatawa a lardin Sichuan ba da dadewa ba, suna gudanar da aikace-aikacen bayar da taimakon kudi ga yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa a kasashen da suke zama. Mai sauraronmu malam Jiang Tianrong, Basiniya mazaunar kasar Amurka, tana koyar da Sinanci a wata makaranta, bayan faruwar girgizar kasa ta Sichuan, tana ta sa himma domin shirya aikin bayar da taimakon kudi. Ta ce, "A gani na, a lokacin da kasarmu ke shan wahala, kuma jama'ar kasarmu ke fama da bala'in, a matsayina na 'yar Sinnawa mazaunan kasashen ketare, ya kamata na yi kokarina kan ayyukan yaki da girgizar kasa da kasarmu ke yi. Tun daga ranar 14 ga wata da dare har zuwa ranar 15 ga wata da safe, na yi ta shirya wata sanarwa, don ba da shawara ga makarantun koyon Sinanci da ke yankinmu don su yi aikace-aikacen bayar da taimakon kudi."

Mai sauraronmu daga kasar Vietnam, malam Le Thi Kim Giang ta ce, "Ban san me zan yi wa yankuna masu fama da bala'i na gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan ba, abu daya kawai da nake iya yi shi ne, na yi kira ga abokaina, da kuma dalibaina, da su bayar da taimakon kudi, ko da yake kudaden ba su da yawa, amma sun nuna sahihiyar zuciya. Na yi imani da cewa, yanzu masu sauraro da yawa suna cike da buri iri daya kamar yadda nake."

A lokacin da kasar Sin da fama da wannan babban bala'in girgizar kasa, mutane daga kasashe daban daban na duniya, suna nuna goyon baya sosai, da bayar da muhimman taimako ga jama'ar kasar, kamar yadda mai sauraronmu daga kasar Iran malam Mohammad Homayoun Mehr ya ce:"a wannan lokaci mai tsanani, zuciyata tana tare da jama'ar kasar Sin."