Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-29 16:52:03    
Labaru masu ban sha'awa na kasar Sin

cri

Mahaifiya Yi Jiefang da hadaddiyar kungiyar mata ta kasar Sin ta daukaka ita a matsayin manyan mahaifa mata na kasar Sin ta ce "kuka ba shi da amfani, ya kamata in cikanta fatan dana. " Yi Jiefang ta yi wannan furuci ne a wani taron da aka yi ran 4 ga watan Maris gabanin ranar mata ta duniya.Yi Jiefang,ita mahaifiya ce da ta ba da duk kaunarta zuwa ga iyalinta da danta Yang Ruizhe. Amma mutuwar dansa ba zata ta sauya alkiblar da ta kafa a rayuwarta. Daga bisani ta mayar da hankalinta kan yaki da kwararowar hamada,wannan ma fatan karshe na danta. Ta kuma ce dana har wa yau dai ba ya rabuwa da mu ba. An haifi Yang Ruizhe a birnin Shanghai a shekara ta 1978,shi abun alfhari da farin ciki ne ga iyayensa. Yayin da shekarunsa ya kai tara,mahaifiyarsa ta tafi Japan domin karo ilimi.mahaifinsa kuma ya bude wani dakin shan magani a can. Yayin da shekarunsa ya kai 13 da haihuwa, Yang Ruizhe ya hadu da iyayensa kuma ya zama dan makaranta.Ya kasance a matsayin gaba wajen karatu, a shekara ta 1998, da ya kai shekaru 20 da haihuwa, jami'ar Chuo wadda ta fi shahara a kasar Japan ta shiga da shi. Yang Jiefang da mijinta sun sa ran fatan alheri ga dansu da zai kammala karatunsa a jami'a. Amma masifa ta bullo a ran 22 ga watan Mayu na shekara ta dubu biyu, an samu hadarin mota da ya kashe Yang Ruizhe. Yi Jiefang ta fashe da kuka ta shiga bakin ciki kwarai da gaske. Ta waiwayo wata rana da ta yi kallon shirye-shiryen talabiji tare da dansa,yayin da suka ga mutanen kasar Sin na yaki da kwararowar hamada a jihar arewa maso yamma ta kasar Sin,danta na cewa yana so ya koma kasar mahaifa bayan da ya kammala karatunsa a jami'a a Japan ya shiga yaki da kwararowar hamada.Wannan abin tunaniya ya sanya mahaifiya ta sake dada karfin zuciya.ta yi murabus da aikinta ta kuma lalashi abokinta da ya bayar da taimako zuwa gare ta da ta kafa wata kungiyar kyautata muhalli ta hanyar dasa bishiyoyi. A shekara ta 2002,Yi Jiefang da mijinta sun sayar da dakunansu na sha magani da na kwana a kasar Japan sun koma kasar Sin daga nan sun shiga yaki da kwararowar hamada.

Bayan da suka yi bincike, sun daddale wata kwangila da gwamnatin gun dumar Hure ta jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta ta dasa itatuwa sama da miliyan daya a cikin shekaru goma da bayar da taimakon wadannan itatuwa zuwa ga manoman wuri bayan shekaru ashirin.

Har wa yau da manoma masu yawan gaske a gundumar Hure ba za su iya mantar da ranar 22 ga watan Afrila na shekara ta 2003,yayin da suka dasa itatuwa masu jurewa sanyi a karo na farko. Kauyawa tsofaffi da yara dukkansu sun je wurin dasa bishiyoyi sun ba da hannu a kai.

Bayan kwanaki 15, an yi ruwan sama a karo na farko a cikin shekara daya da ta shige a gundumar Hure. Manoma 19 da suka dauka nauyin kare itatuwan da aka dasa sun shuka wake a tsakanin itatuwa ba tare da bata lokaci ba.

Bayan rabin wata daban,ciyayi sun fito daga kasa mai rairayi.manoman wurin sun yi iyakacin kokarinsu wajen kare sabbin tsirai tsirai. Ashe abin mamaki shi ne kashi sababin bisa kashi dari na waken da aka shuka sun girma, wannan ba a taba ganin irinsa a kasa mai rairayi ba. Itatuwan da aka dasa sun kyautata muhalli, ciyayi ma suna yaduwa. Bayan haka an dasa itatuwa fiye da dubu dari a wannan bangaren.

A cikin shekaru biyar da suka shige,Madam Yi ta dukufa kanta wajen harkokin inganta jin dadin jama'a. Yunkurin da ta ke yi wajen dasa itatuwa da ciyayi ya jawo jari daga jama'a.Idan ka ba da taimakon kudin Sin Yuan biyar domin renon ice daya, za ka iya kare hamada mai fadin murabba'in mita hudu daga kwararowar rairayi.

Kaunar da Madam ta nuna wa danta da kuma taimakon da ta bayar domin kare muhalli sun girgiza abokanta da manoman gundumar Hure da kuma baki masu dimbin yawa a gida da waje.

A gun wani taron da aka yi kwanan baya, mata da mata iyaye su 1611 da suka zo daga yankin Beilu na lardin Sichun na kasar Sin sun bayar da taimakon kudin da ya kai kudin Sin Yuan 20,955 domin nuna goyon bayan Madam Yi da harkarta ta dasa itatuwa.

Yayin da Madam Yi ta yi jawabi, ta zubar da hawaye domin tunawa da danta. Duk da haka tana da karfin zuciya ta iya jure wahalar da ta sha. Ta yi kira ga mutanen kasa da na waje da su hada kansu wajen dasa itatuwa domin inganta muhalli.

Ta ce "dasa itatuwa miliyan daya da digo daya,burina a duk zaman rayuwata,kuma tunanin danna ne,zan yi iyakacin kokarina duk cika wannan buri da biyan bukatunsa."

Jama'a masu sauraro,wannan shi ya kawo karshen shirinmu na labaru masu ban sha'awa. Mun gode muku saboda kun saurarenmu. Sai wannan lokaci na mako mai zuwa za su sake haduwa da juna.(Ali)