A ran 28 ga wata, zaunanen memban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin kuma shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Wu Bangguo ya je garin Hanwang na birnin Mianzhu da garin Pingtong na gundumar Pingwu da suka fi fama da bala'in girgizar kasa na lardin Sichuan don duba halin da ake ciki, da nuna gaisuwa ga ma'aikatan masana'antu da malamai da daliban makaranta, da nuna jejeto ga jama'a da jami'an wurin da kuma masu aikin ceto da suka zo daga wurare daban daban.
A ran 28 ga wata da safe, Mr. Wu Bangguo ya je masana'antar kera injuna mai suna Dongfang dake garin Hanwang don nuna gaisuwa ga ma'aikata da iyalansu, Mr. Wu ya ce, yana fatan za su hada gwiwa da dukkan ma'aikatan masana'antar don kubutar da ita daga wahalhalu.
Daga bisani kuma, Mr. Wu ya tafi asibitin jama'a da aka gina shi da tantuna na farko na birnin Deyang don gaishe da mutanen da suka jikkata. A ran nan da yamma, Mr. Wu ya je garin Pingtong na gundumar Pingwu, inda ya nuna jejeto ga jami'an garin da na gundumar da sojojin kula da aikin ceto da mutanen da suka fama da bala'in a matsugunan da suke zama cikin gajeren lokaci.
Da maraice, Mr. Wu ya isa cibiyar koyarwa mai suna Changhong dake birnin Mianyang don gaishe da malamai da daliban makarantar Beichuan da suka farfado da ayyukan koyarwa.(Lami)
|