Yau 29 ga wata da safe, an samu nasara wajen bikin yawo da fitilar wasannin Olympics na Beijing a birnin Huainan na lardin Anhui da ke gabashin kasar Sin.
Kafin soma bikin, mahalartan bikin sun yi tsit har na tsawon minti daya domin yin juyayi ga 'yan uwanmu da suka rasa rayukansu a sakamakon girgizar kasa da aka samu a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin.
An soma bikin yawo da fitilar daga filin cibiyar motsa jiki da al'adu na birnin Huainan, kuma an kawo karshen bikin a cibiyar motsa jiki ta birnin. Masu yawo da fitilar da yawansu ya kai 100 sun halarci bikin. Tsawon hanyar da aka bi ya kai kilomita 10, tsawon lokacin kuma ya kai kusan awoyi 2 da minti 30.
A yau da yamma, za a cigaba da yawo da fitilar a birnin Wuhu na lardin Anhui. (Bilkisu)
|