Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-29 14:23:43    
Mr. Umaru Yar' Adua ya dasa wani kyakkyawan harsashi a cikin shekara daya da ya gudanar da harkokin mulki a kasar Nijeriya

cri

Ran 29 ga watan Mayu ya zama rana ta cikon shekara daya da shugaban kasar Nijeriya Mr. Umaru Yar' Adua yake gudanar da harkokin mulki a kasar. Domin taya murnar wannan rana, shugaba Umaru Yar' Adua ya sanar da rana ta 29 ga watan Mayu da ta zama ranar hutu ta duk kasa. Kwararrun kasar Nijeriya suna ganin cewa, a cikin farkon shekara daya da yake gudanar da harkokin mulki, Mr. Umaru Yar' Adua ya kula da harkokin kasar Nijeriya bisa doka, sabo da haka ne, ya dasa wani kyakkyawan harsashi wajen daidaita matsalolin da kasar Nijeriya take fuskanta.

A yayin da Mr. Umaru Yar' Adua yake yin rantsuwar kama aiki na zama shugaban kasar Nijeriya, ya taba bayyana cewa, zai dukufa wajen gina manyan ayyuka, da kyautata tsarin dokokin shari'a na dimokuradiyya, da inganta muhallin zaman lafiya, da kara yaki da cin hanci da rashawa. Shehun malami daga cibiyar nazarin dangantakar da ke tsakanin kasa da kasa Mr. Bola Akinterinwa yana ganin cewa, Mr. Umaru Yar' Adua ya samu wasu nasarori a shekara daya da ta gabata. A cikin wa'adin aikinsa na shekara daya da ta gabata, ya dasa wani sabon harsashi wajen gina Nijeriya, wannan harsashi shi ne tafiyar da harkokin mulki bisa doka. An kori wasu gwamnoni daga mukamansu sakamakon laifuffukan cin hanci da rashawa. A watan Maris na shekarar bana, an tsige ministocin kiwon lafiya da tsaron kasa daga mukamansu bisa laifuffukan satan kudin gwamnati. Wadannan misalai sun bayyana cewa, Mr. Umaru Yar' Adua yana tafiyar da harkokin mulki bisa doka.

Wasu 'yan siyasa sun nuna shakkarsu ga kwarewar Mr. Umaru Yar' Adua wajen gudanar da harkokin mulkin kasa, suna ganin cewa, Mr. Umaru Yar' Adua yana karancin kwarewar yanke shawara a matsayin shugaban kasar Nijeriya. Kawancen jam'iyyun adawa sun bukaci Mr. Umaru Yar' Adua ya yi murabus daga mukaminsa a lokacin da yake tafiyar da harkokin siyasa bayan shekara daya.

Shehun malami daga cibiyar nazarin dangantakar da ke tsakanin kasa da kasa Mr. Bola Akinterinwa ya bayyana cewa, yaya zai samu fahimta da goyon baya daga jama'ar kasar Nijeriya, zai zama wani babban kabulale da Mr. Umaru Yar' Adua yake fuskanta a shekaru 3 masu zuwa a kan hanyarsa ta gudanar da harkokin mulki. Mr. Bola Akinterinwa yana ganin cewa, wannan kalubale ya zo ne daga jama'ar kasar Nijeriya. Sun bukaci fahimtar makoma da shugaban kasar yake jagoranta, sa'an nan kuma za su yanke shawarar ko za su nuna goyon baya gare shi ko a'a. Idan babu kasancewar cikas a tsakanin gwamnati da jama'a wajen yin mu'amala da juna, to, wannan kasa za ta iya samun ci gaba.(Danladi)