Ran 28 ga wata da yamma, bisa labarin da ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayar, bisa umurnin babban ofishin ba da umurni kan fama da girgizar kasa da gudanar da ayyukan ceto na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, an ce, ya zuwa ran 28 ga wata da safe da karfe 12, girgizar kasa da ta auku a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin ya riga ya yi sanadiyar mutuwar mutane 68109 yayin da mutane fiye da dubu 360 suka jikata, kuma mutane kusan dubu 20 suka bace, yawan mutanen da ke fama da bala'in ya kai fiye da miliyan 45.6.
Bisa kididdigar da aka yi, ya zuwa ran 28 ga wata da dare da karfe 12, an riga an ceci mutane da kuma kaurar da su kusan dubu 720, da kuma kubutad da mutane 6541 daga kangaye.
Ban da wannan kuma ya zuwa ran 28 ga wata da safe da karfe 12, yawan mutanen da suka samu jiyya a cikin asibitoci domin jin rauni a cikin girgizar kasa ya kai kusan dubu 85.7, kuma a ciki an sallame su dubu 55.5 daga asibitocin, haka kuma birnin Chongqing da dai sauran larduna 20 sun karbi 'yan lardin Sichuan masu jikata kusan dubu 7.
Bugu da kari kuma ya zuwa ran 28 ga wata da yamma da karfe 12, yawan mutanen kiwon lafiya da aka aika zuwa lardin Sichuan ya kai fiye da 92.1, a cikinsu akwai mutane 200 na kasashen waje.
Ban da haka kuma, kasar Sin ta kebe kudaden Sin Yuan biliyan 19.5 wajen fama da girgizar kasa. Yawan kudade da kayayyakin taimako da kasar Sin ta samu daga gida da waje ya kai fiye da Yuan biliyan 34.7.
|