Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-28 17:25:50    
Kara cin apple da dai sauran 'ya'yan itatuwa zai ba da taimako wajen rigakafin cutar gushewar hankali na tsoffi

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili na "ilmin zaman rayuwa". Ni ce Kande ke gabatar muku da wannan shiri daga nan sashen Hausa na Rediyon kasar Sin. A cikin shirinmu na yau, za mu yi muku wani bayani kan cewa, kara cin apple da dai sauran 'ya'yan itatuwa zai ba da taimako wajen rigakafin cutar gushewar hankali na tsoffi.

Bisa sakamakon wani sabon nazarin da manazarta na kasar Amurka suka yi, an ce, kara cin apple da ayaba da kuma lemon zaki zai iya ba da taimako wajen rage hadarin kamuwa da cutar gushewar hankali na tsoffi.

Manazarta na jami'ar Cornell ta kasar Amurka sun bayar da rahoto a kan mujallar ilmin kimiyya na abinci ta kasar, cewa lokacin da suke yin nazari kan amfanin da ruwan apple da ayaba da lemon zaki ke bayarwa kan kwayoyin jijiya, sun gano cewa, sinadarin polyphenol da ke cikin wadannan 'ya'yan itatuwa suna iya hana toshewar hanyar jini, da kuma ba da kariya ga kwayoyin jijiya daga mummunan sinadari masu guba.

Ban da wannan kuma nazarin ya gano cewa, a cikin wadannan 'ya'yan itatuwa iri uku, an fi samun yawan sinadarin polyphenol a cikin apple, bayansa kuma su ne ayaba da lemon zaki. Manazarta suna ganin cewa, idan mutane suka kara cin wadannan 'ya'yan itatuwa, to za a iya ba da taimako wajen yin rigakafin cutar gushewar hankali na tsoffi.

Bisa labarin da kafofin watsa labarai na kasar Sweden suka bayar a ran 10 ga wata, an ce, masu ilmin kimiyya na kasar sun gudanar da wani bincike cikin dogon lokaci, kuma sun gano cewa, game da mutanen da suka kamu da cutar sukari a lokacin matsakaitan shekarunsu da haihuwa, yiyuwar kamuwa da cutar gushewar hankali ta fi yawa lokacin da suka tsufa.

Kuma an labarta cewa, masu ilmin kimiyya na asibitin Uppsala na kasar Sweden da sauran hukumomin sun gudanar da wani bincike na shekaru 32 ga mutane 2269 da suka kamu da cutar sukari lokacin da shekarunsu ya kai 50 da wani abu da haihuwa. Kuma sakamakon binciken ya gano cewa, a cikin wadannan mutanen da ke kamuwa da cutar sukari, mutane 394 sun kamu da cutar gushewar hankali bisa matsayi daban daban, kuma 102 daga cikinsu sun kamu da cutar gushewar hankali na tsoffi, wanda ya fi wadanda ba su kamu da cutar sukari a lokacin matsakaitan shekarunsu da haihuwa ba kuma sun kamu da cutar gushewar hankali lokacin da suka tsufa yawa har kashi 50 cikin dari.

Wani mai ilmin kimiyya da ya sa hannu a cikin binciken ya bayyana cewa, ta wannan sakamakon binciken, mutane sun fahimtar cewa, ya kamata a mai da hankali a kan cutar sukari, kuma dole ne a fara samun jiyya cikin yakini tun farko, ta yadda sinadarin insulin da ke cikin jikin mutum zai kai wani matsayi kamar yadda ya kamata. In ba haka ba, bayan da aka tsufa, hadarin kamuwa da cutar gushewar hankali zai karu.

Ban da wannan kuma ya kara da cewa, ana bukatar da ci gaba da yin nazari kan dalilin da ya sanya mutane masu kamuwa da cutar sukari suka fi saukin kamuwa da cutar gushewar hankali na tsoffi.